Back to Africa Check

Allurar rigakafi ba zata sa ku zama ‘marasa iri’ ba

“Matuƙar zasu iya mai da ɗan itace mara iri, zasu iya mayar da KU marasa iri ku ma,” wani hoto da ke yawo a Facebook ke cewa. Hoton ya nuno kankana babu ƴan ƴan ƙwallayanta, a saman hoton kuma hannu ne a cikin abun rufe hannu na asibiti da sirinjin allura a hannun. Daga gani dai ana ƙokarin hana yin allurar rigakafin Covid-19 ne.

An turowa Africa Check hoton a matsayin tsokaci, biyo bayan saƙon shirin wayar da kai na #KuSanGaskiyaKuKarɓiAllurarRigakafi ta shafin Twita. 

Tsokacin ya haɗa da wannan bayanin: “Ƴaƴan itatuwan da aka sauya ƙwayoyin halittar su basu da ƴaƴan ƙwallaye. Da zarar kun ƙarɓi allurar rigakafin ku ma zaku zama an sauya ƙwayoyin halittar ku. 

Mallaka da haƙƙin mallakar ƴancin masu yin allurar rigakafi zai ɓace ɓakatatan. Hanyar rage al’umma itace zaku zama marasa iri.” 

Wannan da’awar ƙaryar an tantance ta sau da dama. Alluran rigakafi, waɗanda suka haɗa da alluran rigakafi na mRNA da akayi don kiyaye kamuwa da Covid-19, ba zasu sauya ƙwayoyin halittar mutum ba. Ba za kuma a iya ƙwatanta mutum da ɗan itace ba.

seedless_false

Ku ba ƴaƴan itacen da ba ku da ƙwallayen iri ba ne

Ba sauya ƙwayoyin halitta ne ya ke samar da ƴaƴan itacen da basu da ƙwallaye ba. Kamar yadda kwalejin aikin noma da albarkatun ƙasa ta jami’ar jihar Michigan ta rubuta a shekarar 2019: “A yanzu babu wasu itatuwa marasa iri da aka sauya ƙwayoyin halittar su(GMOs)”.

Itatuwa na samar da ƙwallon iri a halicce, haka nan ana noman marasa iri kamar yadda mutane ke noma kowanne amfanin gona. 

Rashin ƙwallon iri halitta ce, jihar Michigan ta bayyana cewa, “Ɗabi’un gado da ake ɗaukar su ta hanyar folin kuma ƙwayoyin halitta ke riƙe su har sai mahaɗin su ya samu hanyar daidaiton iyayensu, shi ya ke samar da itatuwa masu iri”. Amma maimakon kai tsaye a sauya ƙwayar halittar itatuwa ta DNA, mutane suna kawai zaɓar su shuka itatuwan da ke fitowa ba tare da iri ba.

Za kuma a iya samar da itatuwa marasa iri ta wasu hanyoyin daban. Wasu itatuwa na samar da ƴaƴan itatuwa marasa ƙwallo idan har an gurɓata furensu- amma mutane zasu iya kiyaye afkuwar hakan. A bayanan Encyclopedia Britannica ance ana iya samar da  itatuwan marasa ƙwallo ta hanyar bijirarwa da wasu itatuwa wasu sinadarai, ana hakan kuma tun shekarar 1934. 

Mutane da dama zasu iya zama marasa haihuwa- wanda ke nufin ba zasu iya ɗaukar juna biyu ba. Amma rashin haihuwa ga bil adama ko kusa ba dalilai ɗaya ba ne da rashinta ga itatuwa. Babu wata hujja da ta tabbatar cewa allurar rigakafin Covid-19- ko wasu alluran rigakafin da aka saba yi- zasu iya jawo rashin haihuwa

Alluran rigakafin Covid-19 ba sa sauya ƙwayoyin halittar ɗan adam na DNA

Almara ce ace allurar rigakafin Covid-19 na sauya ƙwayar halittar ɗan adam ta DNA. Wannan da’awar wadda ta fi magana akan alluran rigakafi na mRNA, an sha tantance cewa karya ce, har ma Africa Check sun taɓa ƙaryata ta.

Ɗan aiken RNA, ko mRNA abu ne da ke ɗaukar bayanan ƙwayar halitta. Amma ba ɗaya suke da DNA ba, wanda ke adana ƙwayoyin halittar jini. Sai dai mRNA na bawa jiki umarnin samar da wasu firotin. 

Alluran rigakafin Covid-19 na mRNA na bawa jiki umarnin gina “sifayik firotin”, wani tsari na musamman ga ainihin ƙwayar cutar. Wannan shi zai bawa jiki damar gina sifayik firotin, wanda zai samar da matakan yaƙar ƙwayar cutar

Masana kimiyya a ɗakin bincike na Meedan Digital Health Lab sun ce: “Kafin a sauya ƙwayar halitta ta DNA, dole ne ya zamana an gabatar da ƙwayar halittar jini daga wani abu mai rai an sa a cikin tsakiyar tantanin jikin mutum mai ɗauke da DNA ɗin su.

Shi mRNA da ke jikin alluran rigakafin Covid-19 baya shiga tsakiyar tantanin ya kuma karye cikin awanni 72 ba. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.