Back to Africa Check

Ba haka ba ne, furen St John’s wort da barasa basa maganin ƙurajen herpes

“Na sami saƙo ta dm daga wata mace da take fama da barkewar ƙurajen gaba,” wani saƙo a Instagram ya fara da cewa.

Sai kuma ya bada magani: Furen St John’s wort da barasa.

St John’s wort wani haɗin itatuwa ne da ke da maganin yaƙi da ƙwayar cuta wanda zai taimakawa masu fama da 

matsalar ƙurajen gaba,” saƙon ya ce.

“Wannan magani ne da ake haɗawa da barasa, kuma ana barinsa ya jiƙu har tsahon makonni 6, sai a tace a sha. Za’a iya amfani da barasar 80 proof vodka ( kamar Smirnoff ice vodka ) wajen haɗawa. Saƙon na tare da bidiyon yadda za’a yi haɗin.

herpes_incorrect

Menene ƙurajen herpes ?

Ƙurajen herpes cuta ce da ƙwayar cuta ta herpes simplex ke jawowa. Ƙwayoyin cutar iri biyu ne. HSV-1 tana jawo ƙuraje a baki misalin huciyar zazzaɓi, kuma ana yaɗa ta daga baki zuwa baki. 

Ƙurajen gaba kuma ƙwayar cutar herpes HSV-2 ce ke je jawo shi, duk da cewa HSV-1 ma tana iya jawowa. Matuƙar aka kamu da su ƙwayar cutar na zama a jiki har abada, amma dai basa nuna wasu alamu a jiki. 

Shirin kula da lafiya na National Health System na Britaniya ya ce, a inda aka samun alamun herpes na bayyana a gaba za’a samu “ƙananan ƙuraje ne ke fitowa waɗanda suke fashewa su bar jan buɗaɗɗen tabo a gaba, dubura da matse-matsi; suna sa gaban zafi da ƙaiƙayi; jin zafi yayin yin fitsari” da kuma fitar da ruwa ga mata.

Idan ba’a yi maganin alamun ba zasu iya zama barazanar kamuwa da cutar HIV ga wanda ya ke fama da su. 

Furen St John’s wort ( wanda a kimiyance akafi sani da Hypericum perforatom) itace ne da ya samo asali daga Turai yana kuma fitowa a daji. An daɗe ana amfani da shi wajen maganin matsananciyar damuwa. Amma masana sun yi gargaɗin cewa yawon amfani dashi ka iya rage ƙarfin magungunan asibiti, kamar magungunan cutar HIV dana sankara. 

Shin jiƙa furen a cikin barasa zaiyi maganin ƙwayar cutar herpes?

A guji zafi kuma kar a wanke gaba da wasu sinadarai

“Haɗin furen St John’s wort da barasa bai tabbata ba wajen maganin cutar herpes,” Dr Olajumoke Ogunro, likitar mata ta asibitin haihuwa na Alpha Assisted Reproductive Klinic da ke Lagos ta shaidawa Africa Check. “A halin yanzu babu maganin herpes.”

Ta ƙara da cewa akwai wasu abubuwan da za’a iya yi a gida don rage alamun cutar kamar ƙaiƙayi da raɗaɗi. Kar ku shiga cikin zafi sosai ko cikin zafin rana mai yawa. Gujewa wanke gaba da kayan kula da gaban mace zai taimaka matuƙa,” Ogunro ta ce.

Likitar ta gargaɗi cewa St John’s wort na iya “jawo babbar matsala” idan ta haɗu da wasu magunguna. “Wasu ƙasashen sun haramta amfani da furen, yayin da wasu ƙasashen ke duba yiwuwar hana amfani da shi.”

Kar ku bar alamun ciwo baku nemi magani ba

Idan kuna zaton kuna fama da alamomin herpes, ku nemi ganin likita don baku maganin da ya dace don magance alamomin.

“Idan ba ku sha magani ba zaku iya cigaba da samun cutar akai akai, duk da dai hakan ba kasafai take faruwa ba,” Ogunro ta ce. “Idan baku nemi magani ba za’a ɗau tsahon lokaci kafin alamun su ɓace.”

Haka nan cutar na iya yaɗuwa idan ba’a magance alamun ba. “Idan kuka taɓa ruwan da ƙurjin ke fitarwa kuka taɓa wani sassa na jikin ku, zaku yaɗa cutar a wani sashe na jikin ku.”

 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.