Back to Africa Check

Babu gasar samun izinin shiga ƙasar Amurka ga ƴan Najeriya a shekarar 2021/22- a kiyayi ƴan damfara

Ku karbi damar zama a ƙasar Amurka ku nemi izinin samun katin zama ɗan ƙasa a gasar girin kad,” a cewar wani ɓangare na wani rubutu da aka rarraba a Facebook.

Wasu mamallaka shafukan Facebook a Najeriya sun yaɗa irin wannan da’awar.

Duk kuma suna cewa waɗanda suka ci gasar ta katin zama zasu samu izinin zaman dindindin a Amurka, su kuma samu damar yin aiki a Amurkan.

“A kowacce shekara, Amurka na bada katin zama guda 55,000 ta hanyar shiga gasar,” cewar ɗaya daga cikin rubutun.

Katin zama wanda akafi sani da izinin zama na dindindin, shine abun da ke bawa waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba izinin zama na dindindin da kuma yin aiki a ƙasar.

Amma shin waɗannan rubuce-rubuce akan yadda ƴan Najeriya zasu samu katin zama gaskiya ne? Mun bincika.

visa_lottery

An rufe neman izinin shiga gasar shekarar 2022 tun shekarar  2020

Rubutun na miƙa mutane ga wani shafin wanda shi kuma ya na cewa su rarraba link na shafin da abokansu guda 15 a WhatsApp ko a grup 5 na WhatsApp.

Wannan misali ne na hanyar da ƴan damfara a Facebook ke amfani da ita wajen kara yawan jama’a a shafukansu. A lokuta da dama wannan ne alamar da ke nuna cewa tallan na ƙarya ne.

Link ɗin neman aikin an saka shi a sahun wata hanya da ake amfani da ita don samun bayanan sirri kamar faswod da bayanan katin ku na banki, ta hanyar nuna cewa shafin abin amincewa ne. 

Da muka binciki yanar gizo akan“2022 US lottery programme” ya kai mu bureau of consular affairs, wanda sashe ne na jihar Amurka

Lokacin rigistar shiga gasar samun takardar izinin shiga ta 2022 shine tsakanin 7 ga watan Octoba zuwa 10 ga watan Nuwamba 2020.

Gasar ba’a buɗe ta ga ƴan Najeriya ba

Bugu da ƙari, ƴan Najeriya basa cikin jerin rukunin da zasu iya shiga gasar ta shekarar 2022, kamar yadda dokar shiga gasar take a hukumance. 

Saboda an ƙirƙiri shirin ne don “ya samar da dama ga masu son suyi ƙaura zuwa Amurka, waɗanda suka fito daga ƙasashen da ba’a cika samun masu shiga Amurka daga ƙasashen ba.

Najeriya na cikin rukunin da ke yawan shiga Amurka. Waɗannan sune ƙasashen da sama da mutane 50,000 suka yi ƙaura zuwa Amurka a shekaru biyar ta dalilin iyalin su ko karatu.

A kiyayi shafuka na bogi

A watan Yuni na shekarar 2021, ofishin jakadanchi Amurka da ke Najeriya ya gargaɗi jama’a masu neman izinin komawa Amurka da zama, da su kiyaye da shafukan yanar gizo na ƙarya.

“Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya na sane da shafuka da saƙonni da ake ta yaɗawa da ke tallan gasar samun izinin zama a Amurkam. Duka waɗannan na ƘARYA ne!” Saƙon na Twita ya ce.

Sun kuma sanar da hanya mafi sauƙi wajen gane irin waɗannan shafuka na bogi: Adireshin dake da .gov ne kawai sahihiyar hanyar samun labaran da suka danganci bizar na gaskiya.”

 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.