Back to Africa Check

Haɗa nau’ukan abinci, ganyayyaki da itatuwa baya maganin ciwon amosanin gaɓoɓi

Wani rubutu da ke yawo a Facebook a Najeriya ya bada shawarar “ maganin amsonin gaɓoɓi”, aka kuma jero nau’ukan abinci na yau da kullum kamar inibi, lemon tsami, zuma, citta da tafarnuwa a matsayin masu warkarwa.

Rubutun na haɗe da inda za’a latsa a shiga wani shafi da ya kira kansa da “ Africa’s No 1 herbal medicine shop”, wanda ya ke ɗauke da rubutu akan makamanciyar da’awar.

Amosanin gaɓoɓi, wanda akafi kira da awoka, awuka da aromoleegun a harshen Yarabanci, cuta ce da ke jawo kumburi, raɗaɗi da ƙagewar gaɓoɓi. Ire- iren amosanin gaɓoɓin da aka fi sani sun haɗa da austiyoraitis da romotoyad. 

Austiyoraitis shi yana afkuwa ne saboda yawan shekaru, yayin da rumatoyad ya fi yawa ga mata, a kuma ƙasashen da suka cigaba, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce.

Shin da gaske wannan haɗi na maganin amosanin gaɓoɓi?

arthritis_

 

Magani na danganta da musabbabin ciwo

John Onuminya, Farfesa a fannin kula da ƙashi na jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, kudancin Najeriya, ya shaidawa Africa Check cewa,” babu hujja a kimiyance” da ta tabbatar da ingancin da’awar da aka rubuta a Facebook.

“ Sababin ciwon amosanin gaɓoɓi na da yawa, don haka zaiyi wuya a ce ga maganin cutar guda ɗaya,” Farfesan ya ce. “ Babban abun da masu fama da ciwon suka fi kuka da shi, shi ne raɗadin ciwo, kuma babu wani abu daga cikin waɗannan kayan haɗi da zai maganin raɗaɗin.”

Hanyar da kawai wannan haɗi zai yi tasiri shine abun da ake cewa tasirin filasibo.  Ma’ana lokacin da mara lafiya ya yarda cewa wannan abun zai rage masa raɗadin ciwo- duk da cewa a zahiri haɗin babu abun da yayi.

Omuninya ya shawarci masu fama da ciwo da su je su ga likita.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.