Back to Africa Check

Haɗi mara tushe: Ɗakin gwaji na Wuhan ba mallakin GlaxoSmithKline ba ne, bai kuma mallaki Pfizer ba

“ Ɗakin gwaji na ƙasar Sin da ke Wuhan mallakin GlaxoSmithKline ne,” abun da ke ƙunshe kenan cikin wani saƙo da ke ta yawo a kafar Facebook.

Rubutun ya cigaba da cewa, kamfanin yin magunguna na GlaxoSmithKline ne ya mallaki kamfanin Pfizer, wani kamfanin yin magunguna. Kamfanin Pfizer ya fitar da rigakafin koronabairas, wacce ta samo asali daga Wuhan, China a ƙarshen shekarar 2019.

Rubutun ya haɗa waɗannan kamfanunnuka da wasu manya da ake shirya makirce- makirce akan annobar Covid-19 da sunayen su, waɗanda suka haɗa da shugaban kamfanin Microsoft Bill Gates da Dr Anthony Fauci, shugaban cibiyar cututtuka masu yaɗuwa ta Amurka.

“ Maƙarƙashiyar makirci ko arashi?” abun da rubutun ya fara ƙunsa.

Ya nuna cewa mutanen, kamfanunnukan da hukumomin da aka ambata na da hannu wajen annobar Covid-19. Rubutun ya nuna cewa Pfizer ne suka ƙirƙiri allurar rigakafin cutar. Shin da gaske duk waɗannan abubuwan na da alaƙa da juna?

Wuhan_false

 

Da’awar ta yi wata bakwai kuma har an tantance cewar ƙarya ce

Babu dai tabbacin sanda aka fara yaɗa da’awar, amma Africa Check ta samo irin da’awar, wadda ta gano cewa an fara yaɗa ta a watan Nuwanbar 2020. Masu tantance labarai na Reuters sun tantance ta a watan Disemba har sau biyu, haka ma Australian Associated Press sun tantance ta.

Rubutun ya ta’allaƙa akan cewa annobar Covid-19 ta “samo asali ne daga wani ɗakin gwaji da ke Wuhan”, wadda aka alaƙanta ta da GlaxoSmithKline da Pfizer. Abun ba haka ya ke ba.

Da farko dai, babu hujjar da ta tabbatar da cewa Covid-19 ta “samo asali daga ɗakin gwajin ƴaƴan halitta a Wuhan”. Masana sun yi watsi da wannan batu, sun dai yadda cewa ƙwayar cutar ta yaɗu ne daga jamage zuwa ga ɗan Adam ta hanyar nau’in wata dabbar.

Babu wata alaƙa tsakanin cibiyar ƙwayoyin cuta da ke Wuhan da GSK. Cibiyar bata ambaci GSK a matsayin abokan huldar ta ba a shafinta na yanar gizo. Shafin dai ya ce cibiyar Chinese Academy of Sciences ne suka ƙirƙiri cibiyar kuma suka mallake ta.

Haka nan GSK ba ita ta mallaki Pfizer ba. A shekarar 2018, kamfanunnukan biyu sun amince zasu haɗe rassan su da ke kula da lafiyar masu amfani da abun  da su ke sarrafawa, ta yadda kashi 68% zai zama mallakin GSK. Baya ga haka kowanne daga cikin su zaman kansa ya ke, sannan haɗakar bata haɗa da ayyukan bincike da cigaba ko rigakafi, ko rassan kowanne daga ciki ba.

Wannan itace kawai alaƙar da rubutun na Facebook  ya bayar ba dai dai ba. Da yawa daga cikin alaƙoƙin da aka ambata basu da tushe, yayin da sauran ke yaudarar mai karatu. Ga dai duka alaƙar da rubutun ya ambata da hujjojin da Africa Check ta binciko( waɗanda sau tari suka kasance saɓanin abun da suka faɗa).

Akwai mahaɗun da ba’ayi amfani da su ba

 Ba Dr Anthony Fauci ba ne ya ƙirƙiri cibiyar ƙwayoyin cuta ta Wuhan. Kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya yi bayani, mafi kusanci da gaskiya a wannan bayani shine cewa tsakanin 2015 da 2019 an bawa cibiyar tallafi daga wata ƙungiya, wadda US National Institute of Health ke tallafawa wadda cibiyar kula da lalurar alaji da cututtaka masu yaɗuwa da Fauci ke jagoranta ke ciki.

 

FB real

 

Duka BlackRock da Vanguard na da jari a GSK ( BlackRock na da kashi 7.5% na jari), wadannan biyu ne daga cikin kamfanunka 1,528 da ke da jari a GSK. Don haka ba za’ace “BlackRock ke tafiyar” da GSK ba, sam ba haka ba ne.

Kuma ba BlackRose ne ke sarrafa kuɗaɗen Open Society Foundations ba. Mamallakkin Open Society, George Soros ke bawa gidauniyar kudi. Babu kuma hujjar da ta nuna cewa hukumar “na wa French AXA aiki”.

Kamfanin inshora mallakin ƙasar Faransa AXA bai ambaci Open Society Foundations ba acikin taswirar tsarin ƙungiyar ba, sannan babu hujjar cewa sun karɓi tallafi daga Open Society ko wani tallafi na daban.

A shekarar 2006, AXA ta mallaki kamfanin Swiss Company Winterthur, wanda rubutun na Facebook ya ce Soros ne ya mallaka.

Hukumar US Securities Exchange ta na tattara bayanan masu rijistar kamfani har 3000 a kullum a laburaren tattara bayanai, nazari da bincike (Edgar).

Wannan ya nuna cewa, duk da cewa akwai alaƙa tsakanin Vanguard da BlackRock( bayanan kwanan nan na nuna BlackRock ya mallaki kashi 14.6% na jarin American Vanguard Corporation), Vanguard bata da alaƙa da Allianz SE( wadda ke da hediƙwata a Jamus), sannan Allianz ta bayyana AXA a matsayin abokin gasarta  (ba reshenta ba).

BlackRock ya mallaki sama da kashi 5% na jarin Microsoft, hakan na nufin (kamar yadda rubutun na Facebook ya ambata) a matsayin “ babban mai hannun jari”. Amma rubutu bai yi dai dai ba da ya kira Microsoft “mallakin” wanda ya ƙirƙire shi, Bill Gates. Gates ba shine mafi rinjaye a cikin waɗanda suka mallaki Microsoft ba tun 2014, bama yana cikin masu bada shawara a Microsoft.

Gates ba ya cikin masu hannun jari a Pfizer, amma gidauniyar Bill da Malinda Gates ta bawa Pfizer tallafi a 2019 don yin bincike a kan cutar Nimoniya, a cewar bayanin harajin gidauniyar. Haka nan, Gates ba shi ne ya fi bada tallafi mafi tsoka ba ga hukumar lafiya ta duniya, amma gidauniyar Gates ce ta bada tallafi mafi tsoka ga WHO a ƙarshen shekarar 2020.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.