Back to Africa Check

Har yanzu babu maganin warkar da ciwon HIV

Wani saƙo da ke yawo a Facebook a ƙarshen watan Junin 2021 na iƙirarin cewa yanzu an samu maganin warkar da ciwon HIV. Saƙon yace, kawai; “Maganin warkar da HIV ya fito.”

Bai yi wani ƙarin bayani ba ko faɗar tushen bayanin ba.

Ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki, ko HIV, na kaiwa fararen ƙwayoyin halittar jini hari, musamman ƙwayoyin halitta na CD4, sai su raunana garkuwar jiki. Ana yaɗata ta hanyar haɗuwar jinin mai cutar dana mai lafiya ko haɗuwar ruwan jiki, lokacin saduwar jima’i ko daga uwa zuwa ɗa yayin haihuwa ko shayarwa.

A shekarar 2020, ƙasar Afrika ta Kudu na da ƙiyasin masu ɗauke da cutar har mutane miliyan 7.8. Wanda ya ɗan haura kashi 13% na jama’ar ƙasar.

Cutar ƙarancin adadin ƙwayoyin halitta masu garkuwa daga cututtuka a jiki, ko AID, ita ake nufin da mafi tsananin cutar HIV. Sai dai kuma da amfani da magungunan da akafi sani da antiritorobairal terapi ko ART, masu fama da cutar HIV basa kaiwa matakin da cutar zata zama AIDS.

Amma an samu maganin warkar da cutar HIV? Mun bincika.

‘Babu sahihin maganin warkar da HIV’- CDC

A cewar hukumar kiyaye yaɗuwar cututtaka ta Amurka, ko CDC, a halin yanzu babu wani sahihin maganin warkar da HIV. 

Za’a iya kula da HIV ta hanyar amfani da magungunan ART, waɗanda suka kasance haɗin magunguna ne da za’a ringa sha kullum. Waɗannan magunguna zasu rage yawan HIV a jiki, wato bairal lod, su kuma ƙara yawan CD4.

Wannan na bawa jiki damar samar da garkuwar jiki don yaƙi da ƙwayoyin cuta. Ya rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu. Lokacin da ba’a samu samuwar ƙwayar cutar ba, ba za’a iya yaɗa ƙwayar cutar HIV ga abokan zama ta hanyar yin jima’i ba tare da amfani da abun kariya ba, hakan ma zai kiyaye yaɗuwar cutar daga uwa zuwa ɗa.

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta na bada ARTs ga masu ɗauke da cutar HIV tun 2003.

Amma ART baya warkar da HIV.

hiv_cure_false

An yi gwajin alluran rigakafin HIV, amma ba’a amince da su ba tukunna

Kamfanonin haɗa magunguna na Moderna da na Johnson & Johnson sun bayyana waɗanda za suyi gwajin alluran rigakafin cutar HIV da su.

Moderna sun bayyana a ranar 18 ga watan Agusta 2021 cewa sun shirya don gwajin allurar rigakafin HIV akan yan adam. Sun yi amfani da fasahar mRNA irin wadda akayi amfani da ita wajen yin allurar rigakafin Covid-19.

Johnson & Johnson sun kammala matakai biyu na gwajin waɗanda za’a yiwa allurar rigakafin a watan Agusta na 2021. An yi gwajin a ƙasashen Afrika na cikin hamada a kan mata waɗanda suke cikin barazanar ɗaukar ƙwayar cutar amma allurar rigakafin “bata samar da isassiyar kariya” daga ƙwayar cutar HIV ba.

A halin yanzu babu allurar rigakafin HIV. Sannan allurar rugakafi zata kiyaye ɗaukar cutar ne ba zata warkar da cutar ba.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.