A ranar 15 ga watan Fabrairun 2021 aka bayyana masaniyar tattalin arziki ƴar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar babbar daraktar cibiyar kasuwanci ta duniya(WTO).
Jimkaɗan bayan naɗin nata, wani hoton wata yarinya ya fara yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya da cewa hoton sabuwar daraktar ce tana ƙarama.
Wasu na yaɗa hoton tare da hoton babbar darakta na yanzu.
Mun bincika ko wannan batu gaskiya.
Hoton ya samo asali daga ƙasar Ghana tun 2014
Kafar tantance hoto ta Google reverse image search ta bayyana mana asalin hoton, wanda aka fara sa shi a yanar gizo a wani shafi mai suna Fresh Wall Street a shekarar 2014. Ta kuma nuna cewa hoton mai ɗaukar hoto Allen Coleman ne ya ɗauki hoton.
Coleman ya shaida mana cewa ya ɗauki hoton a ƙasar Ghana a shekarar 2014, ya ƙara da cewa: “ Hoton na wata yarinya ce ƴar ƙasar Ghana. Babu abun da ya haɗa hoton da babbar daraktar WTO.”
Mun tambaye shi ko Okonjo-Iweala ce a cikin hoton, ya ce: “Sam, ba ita bace.”
Africa Check ta sake bincikar hoton ta hanyar amfani da InVID WeVerfy. In da ta tabbata an ɗauki hoton a ranar 28 ga watan Juli 2014, aka kuma gyara shi kwana biyu bayan ɗaukar sa.
Okonjo-Iweala dai an haife ta a ranar 13 ga watan Juni a shekarar 1954, shekarunta 60 a shekarar 2014.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment