Back to Africa Check

Jiƙa goba da sawasop ba zai cire sis a ƙwan mahaifa ba, ya tsaftace bututun cikin mahaifa ko kuma ƙara yawan maniyyi

Wannan haɗin na ganyen goba da sawasop na da amfanin wajen wanke mahaifa, magance sis na ƙwan mahaifa, taftace bututun mahaifa, ya kuma taimaka wajen ƙara yawan maniyyi,”abunda  saƙon da aka rarraba a Facebook ke cewa. 

“ Wannan haɗin na aiki sosai!!!”

Saƙon ya ce a wanke ganyen goba dana sawasof cikin tafin hannu, a zuba a cikin ruwa lita guda a tafasa, a tace. 

“ A sha rabin kofi da ɗumi safe da yamma.”  Daga cikin irin abun da haɗin zai haifar har da saukar da jinin da ya hau.

 Wannan haɗin zai wanke mahaifa, ya cire sis daga ƙwan mahaifa, ya buɗe bututun mahaifa, ya kuma ƙara yawan maniyyi? Mun bincika.

Guava_soursop_cure

 

Fahimtar yadda cutar ta ke

Wajen samar da ƙwan mahaifa wasu abubuwa ne guda biyu masu kama da gyaɗa a kowanne gefe na mahaifa. A jikin babbar mace duk wata suna fitar da ƙwayoyin halitta na homons, sannan su samar da ƙwai.

Shi kuwa sis na wajen samar da ƙwan mahaifa, wata jaka ce ta ke fitowa a jiki  mai cike da ruwa.

Shi kuwa bututun mahaifa yana haɗa mahaifa ne da wajen samar da ƙwai. Maniyyi ke ƙyanƙyashe ƙwai  cikin ɗaya daga cikin bututun, sannan ya ɗauki ƙwan zuwa mahaifa. Idan ɗaya ko duka bututun suka toshe, mace kan samun wahala wajen ɗaukar juna biyu.

Abun da ake kira ektofic shine lokacin da ƙwai ya zauna a bututun har ya fara girma bai wuce cikin mahaifa ba. Wannan lalurar barazana ce ga rayuwar mace, don bututun zai fashe ya farar zubar da jini ta ciki.

Ƙarancin maniyyi kuma shine lokacin da namiji ke gaza samar da maniyyi miliyan 15 lokacin da ya kawo yayin saduwa. Rashin maniyyi na nufin kwata-kwata namiji baya fitar da maniyyi bayan ya kawo yayin saduwa. 

A daure a ga likita

“ Bamu da wata masaniya cewa wannan haɗi zaiyi maganin waɗannan cututtuka; sam babu ta yadda za’ayi,” Nimi Briggs, Farfesa akan mata da lalurar juna biyu na jami’ar Port Harcourt, ta shaidawa Africa Check.

Matan da ke fama da sis a wajen yin ƙwai na mahaifa ko bututun mahaifar ya toshe, su je su ga likita don gwaji da basu maganin da ya dace.”

Hukumar kiwon lafiya ta Britaniyya ta ce ‘ a lokuta da dama, sis yana bajewa da kansa bayan ƴan watanni. Za’a kuma ɗauki hoton cikin ta hanyar sikanin a tabbatar.” Bututun da suka toshe na buƙatar ayi aiki don a gyara su.

Sulayman Alege Kuranga, Farfesa akan lafiyar mafitsara na tsagayar kimiyyar kiwon lafiya ta jami’ar Ilorin, a Yammacin Najeriya, ya shaidawa Africa Check cewa wannan haɗin magani ba zai ƙara yawan maniyyi ba. “ Sam, babu wani abu kamar hakan, babu hujjar da ta tabbatar da hakan a kimiyyance.”

Ya shawarci mazan da ke fama da lalurar da su je ga ƙwararru masana kiwon lafiya don samun kulawar da ta dace.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.