Back to Africa Check

Kashi ‘90%’na ƙaton ciki ba ya nufin’ alamu ne na ciwon hanta- ana buƙatar cikakken bincike

“Alamu na farko ga kitsen hanta ko hantar da ta kumbura shi ne potty belle”, abun da wani saƙo da aka saka a Facebook Najeriya ke cewa. Yana nufin “ƙaton ciki.”

Ƙaton ciki na nufin ciki zagayayye. Amma saƙon na cewa masu ƙaton ciki na da kaso 90% na yiwuwar iya kamuwa da cututtukan kitse da na kumburin- hanta. 

Matuƙar kana da ƙaton ciki kana da kashi 90% na yiwuwar samun kitsen hanta”, saƙon ya ce.

Da gaske masu ƙaton ciki na da kashi 90% na yiwuwar kamuwa da cutar kitsen hanta? Mun bincika. 

Potbelly_Incorrect

Ciwon hanta na buƙatar gwaje-gwaje kafin a tabbatar da kamuwa da shi

Kitsen hanta na nufin taruwar kitse a jikin hanta. Hanta itace sashen cikin jiki ma fi girma. (Fata itace sashen jiki mafi girma, amma ita a wajen jiki take ba a ciki ba.) Hanta na daga gaban ciki daga ƙasan huhu, amma a saman tumbi. Abun da ake kira da ciki, na can ƙasa ƙarƙashen hanta da tumbi. 

Ciwon kitsen hanta ba shi da alaƙa da yawan shan barasa, ana kuma kiran sa da ciwon kitsen hanta wanda bashi da alaƙa da barasa. Yayin da kuma ciwon kitsen hanta wanda barasa ke jawowa, kamar sunan sa yawan shan barasa ke haddasa shi. 

Sauran cututtukan da kan iya jawo ciwon hanta su ne ciwon suga nau’i na biyu, matsananciyar ƙiba, ciwon hawan jini da hauhawar kitse a jiki. 

Dr Joanah Ikoba wadda babbar likitar yara ce da ta ƙware akan cututtukan cikin ciki da cututtukan jini kuma babbar malama a jami’ar Najeriya da ke Calabar, ta shaidawa Africa Check cewa girman ciki ba hanya ce ta tabbatar da kamuwa da kitsen hanta ba ko sauran cututtukan hanta ba. 

Ikobah ta ce ana gane ciwon hanta bayan anyi gwaje-gwaje masu dama, waɗanda suka haɗa da yin hoton sautin ciki wato ultrasound a ciki da gwaje-gwajen jini da kuma hoton sautin ciki na faibirosikan

Sauran gwaje-gwajen sun haɗa da gwajin da ake ɗaukar tsoka wato biopsy na hanta da kuma ɗaukar hoton ciki don bincike wato MRE

“Ba dai-dai bane ace mutum yana da kitsen hanta ko wani ciwo da ya danganci hanta don kawai mutum nada ƙaton ciki,” Ikobah ta shaida mana. “Duk da cewa matsananciyar ƙiba na iya jawo kitsen hanta, amma marasa ƙiba za’a iya gano suna da ita.”

Ta ƙara da cewa maganin kowanne irin ciwon hanta ya danganta da abun da bincike ya nuna. 

Hanta mai kitse da wadda ta kumbura ana iya gano su ne kawai ta hanyar dubawa da kuma gwaje-gwaje. Ba lalle ne mutune masu ƙaton ciki ya zama suna da ciwon hanta ba. Haka nan mutanen da basu da ƙaton ciki zasu iya samun ciwon hanta.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.