Back to Africa Check

Koka- kola basa bada kyautar kuɗi ga ƴan Najeriya- ayi hankali da masu damfara

Wani saƙo da ke yawo a WhatsApp a Najeriya na iƙirarin cewa koka- kola na bada kyautar kuɗi don bikin murnar cikar kamfanin shekaru 135 da buɗewa.

Saƙon wanda ba’a rubuta shi da kyau ba, ya na cewa: “ Bikin cikar Koka- Kola shekaru 135! Za ku ci 416464kyauta. Na samu nawa.”

Saƙon ya haɗa da wajen da za’a latsa a faɗa wani shafi da ba’a tsara shi da kyau ba, inda ake buƙatar mutane su amsa tambayoyi guda uku. 

Hakan dai zai yi wuya, shin gaskiya ne  Koka- Kola na bada kyauta?

Cocacola_Fake

Ku kiyaye bayanan kan ku

Koka- Kola tayi bikin cikarta shekaru 135 a watan Mayun 2021. Rubutu irin wannan za’a same shi ne a shafukan  kamfanin Koka- Kola Najeriya na Instagram da Twitter.  

Ba mu samu wani saƙo makamancin wannan ko na wata gasa ba daga shafin Koka- Kola ko shafukan kamfanin na sada zumunta ba. 

Zai yi wuya a ce kamfani mamallakin biliyoyin daloli a faɗin duniya zai bada wata garaɓasa a shafin yanar gizon da ba mallakarsa ba ko ta saƙon WhatsApp. 

Africa Check ta taɓa tantance da’awa makamanciyar wannan da ke amfani da manyan sanannun sunayen wajen samun bayanan jama’a na sirri.  Domin samun  karin bayani a karanta rubutun mu akan hanyoyin gano damfara a Facebook

 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.