Back to Africa Check

Ƙwaiduwar ƙwai da gishirin beza basa sauƙaƙa ciwon gwiwa da na gaɓoɓi

“ Hanyar magance ciwon gwiwa da na gaɓoɓi ta asali,”abun da ke ƙunshe a cikin wani saƙo da ke yawo a Facebook a Najeriya.

Saƙon na iƙirarin cewa haɗa ƙwaiduwar ƙwai da gishirin beza zai yi maganin wannan ciwon.

A kaɗa ƙwaiduwar ƙwai har sai ta koma fari, sai a sa gishirin beza a gauraya su. Sai a sa haɗin a auduga, a dora akan inda ya ke ciwo sai a saka bandeji mai roba a ɗaure wajen. A bar shi na tsahon awanni 2, za’a iya yin hakan har sau 4 a wuni guda.”

Gishirin beza, sinadari ne na maganesiyon, solfo da oksijin wanda ke da ɗaci kuma launin fari.

Gaskiya ne wannan haɗin zai yi maganin ciwon gwiwa ko gaɓoɓi?

Knee_remedy

 

 

Babu tabbacin hakan a kimiyance

Ciwon gwiwa, cuta ce da aka san ta. Abubuwa da dama kan jawo ta, kama daga rauni da ciwon amosanin gaɓoɓi. Ciwon amosanin gaɓoɓi shine lokacin da gaɓoɓi suka kumbura. 

Akwai magungunan ciwon gwiwa da na gaɓoɓi, wanda suka danganta da abun da ya jawo su.

“ Kwanannan na ci karo da da’awar, amma nayi watsi da ita, babu hankali a ciki, “ Farfesa Chike Anibeze, ƙwararre a fannin sanin jikin ɗan adam na kwalejin magunguna ta jami’ar jihar Enugu ya shaidawa Africa Check. 

Anibeze ya ce bai taɓa cin karo da wani bincike da akayi akan cewa ƙwaiduwar ƙwai da gishirin beza na maganin ciwon gaɓoɓi ba.

“ Kayan haɗin basa shafar gwiwa ko gaɓoɓi. Shawarar da zan bayar itace duk mai fama da wannan ciwo, ya je ya ga likita. Likitan zai gano musabbabin ciwo ya bada maganin da ya dace.”

 

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”. What should you do? First, don't delete!

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Facebook’s third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Further Reading

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters