Back to Africa Check

Oby Ezekwesili bata ce sace yan matan Chibok da fafutukar #AdawoManadaƳanmatanmu‘ shirya su’ aka yi don taimakawa Buhari ya kada Jonathan a zaɓen 2015

Dr Oby Ezekwesili, fitacciyar malama kuma yar siyasa wadda ta riƙe babban aiki a babban bankin duniya da hukumar fayyace gaskiya ta ƙasa da ƙasa, ta ce garkuwa da yan matan makarantar Chibok guda 276 da Boko Haram sukayi a shekarar 2014- da kuma kamfen na #AdawoMamanaDaƳanmatanmu  don a kubutar da su- an” shirya shi ne don a ɓata” shugaban kasa na wannan lokacin, shugaba Goodluck Jonathan

A ƙalla, wannan na daga cikin wasu kalamai da aka alaƙantasu ga Ezekwesili, aka buga a Facebook a ranar 15 ga watan Mayu 2021 aka kuma yaɗa shi sosai. Sai dai rubutun na ƙarya ne. Ezekwesili bata faɗi haka ba. 

Rubutun na nuna hoton Ezekwesili a gefen hoton shugaba Muhammadu Buhari, shugaban ƙasa mai ci a yanzu. Buhari ya kada Jonathan a zaɓen 2015.

“ A kiyaye lokacin da ake aiki tare da Fulani, saboda manufar su daban da abun da kuke tunani,” kalaman da aka alƙanta ga Ezekwesili suka fara cewa. Buhari bafulatani ne, waɗanda ƙabilar jama’a ne da suka watsu a cikin ƙasashen yammacin Afrika da dama.

A watan Afrilun 2014, ƙungiyar masu tada ƙayar baya ta Boko Haram sun sace yara ƴan mata 276 daga ɗakunan kwanan su a wata makaranta da ke garin Chibok, na jihar Borno a arewa masu gabashin Najeriya.

Ezekwesili ce ta jagoranci kamfen na  fafutukar #AdawoMamanaDaƳanmatanmu, tare da ƴar siyasa Hadiza Usman. Fafutukar ta samu goyan baya a faɗin duniya.

Kalaman ƙaryar da aka alaƙanta su ga Ezekwesili na cigaba da cewa: “ Nayi aikin ‘dawo mana da ƴan matan mu’ tare da Hadiza Bala Usman a shekarar 2014.”

Kalaman sun haɗa da zargin da ke cewa, “ Ban san cewa jagoran Fulani ne suka turo [Usman] don ɓatawa Goodluck Jonathan suna ba don Muhammadu Buhari ya lashe zaɓe ba.”

Ta ƙara da cewa: “ Jim kaɗan bayan zaɓen, sai ta bar aikin fafutukar, aka bata muƙamin MD ta hukumar tashoshin ruwa ta Najeriya(NPA).”

Abu mafi ɗaukar hankali a ƙarshen kalaman da aka alaƙanta ga Ezekwesili, shi ne: “ Yanzu na tabbatar ‘ Sace ƴan matan Chibok’ an shirya shi ne don ɓatawa Goodluck Jonathan suna don Muhammadu Buhari ya lashe zaɓe.”

Oby_false

 

A dawo da ƴan mata- badan a samu wasu maki a siyasan ce

Gwamnatin Buhari ta bawa Usman muƙamin daraktar gudanarwa ta hukumar tasoshin ruwa ta Najeriya. A watan Mayun 2021 aka dakatar da ita daga muƙamin. 

Africa Check ta bincika don samun ko wasu kafofin yaɗa labarai masu inganci sun wallafa wannan kalamai na Ezekwesili, amma bata samu ba.

Mai magana da yawun Ezekwesili, Ozioma Ubabukoh a wata sanarwa da ya fitarwa manema labarai, wadda ya aikowa Africa Check a saƙon Imel, sanarwar ta ce kalaman da aka wallafa ƙarya ne. 

“ Ezekwesili bata faɗa ba, kuma ba zata taɓa faɗar waɗannan kalamai masu ban tsoro ba akan kamfen ɗin da ta jagoranta cikin tausayawa don ceto yan matan da aka sace a Chibok”, in ji sanarwar

“ Ezekwelisi ta fara ɗaukar matakin shari’ah akan kafafen yaɗa labaran da kuma ɗaiɗaikun jama’ar da suka wallafa waɗannan kalaman ƙarya da aka alaƙanta ta da su. Waɗanda kuma ta ce su ɗin  marasa son ganin gazawar gwamnati a 2014 wajen hanzarta ceto ƴan matan Chibok.”

Ubabukoh ya ƙara da cewa, kamfen ɗin #AdawoManaDaƳanmatanmu “ba’a yi shi don ɓatawa kowa suna” a siyasance ba.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.