Back to Africa Check

Saiwar Afrikan baizil, jan dodon koɗi da ganyen lemongiras basa maganin basir

“ Maganin basir mai inganci (basir na ciki da na waje),” ƙunshe  a cikin wani saƙo da ke yawo a wani shafin Facebook Najeriya. Saƙon na iƙirarin cewa haɗa saiwar Afrikan baizil, jan dodon koɗi da ganyen lemongiras zai kawar da basir. 

Saƙon ya bayyana yadda za’a yi haɗin da yadda za’a sha, inda saƙon ke ƙarewa da: “ Ga basir na waje, a haɗa gari da man ja, sai a sa a dubura don rage raɗaɗin, sai a mayar da abun da ya fito. Fatan samun lafiya cikin gaggawa.”

Wannan haɗin da gaske zaiyi maganin basir? Mun bincika.

Haemorrhoids_incorrect

 

Ana maganin sa da magunguna da kuma aiki

Basir, na samuwa ne lokacin da jijiyoyin dubura ta ƙasa suka kumbura. Basir na ciki shine kumburin jijiyoyin dubura ta ciki, yayin da basir na wajen kumburin yana faruwa ne a ƙasan fatar dubura.

Mun tuntubi Casimir Omuemu, Farfesan magunguna a jami’ar Benin da ke Kudancin Najeriya, ko wannan haɗi zai yi aiki. 

“ Sam baya aiki,” ya ce. “ Wannan ba’a amince da shi ba, don magani a kimiyyance.”

Ya ƙara da cewa akwai hanyoyin maganin basir da suka haɗa da bada magani ko yin aiki.

“ Ana bada magunguna don hana basir ɗin zubar jini, rage kumburi da kuma hana raɗaɗi. Mangunguna kawai basa maganin basir. Za’a iya yin aikin tiyata ko yin aikin zamani na endoscopy don magance basir ɗin.”

Ya yi bayanin cewa yayin endoscopy ana sa roba a ɗaure basir ɗin ko kuma ayi amfani da ɗumi a ƙone basir ɗin.

Omuemu ya ƙara da cewa, duk lokacin da aka samu basir duk abun da akayi amfani wajen magani ba zai hana basir ɗin dawowa ba bayan wasu shekaru, musamman idan ba’a kula an kiyaye musabbabin basir ɗin ba, musamman matse bayan gida. 

Ya ce hanya mafi sauƙi ta kiyaye basir bata wuce kiyaye barin bayan gida yayi tauri, ta hanyar yawan cin kayan lambu da kuma shan ruwa da yawa. A kuma guji matse bayan gidan yayin da aka zo yin sa.

Ya ƙara da cewa a kiyaye amfani da magungunan gargajiya don zasu iya jawo rauni, musamman waɗanda ake sawa a dubura. 

Adegboyega Fawole, Farfesa akan mata da  kula da lalurar masu juna biyu  a jami’ar Ilorin, Yammacin Najeriya,yace akwai yiwuwar mata zasu kamu da basir bayan haihuwa. 

“ An fi samun sa bayan haihuwa, saboda matsin ciki da kuma nishi yayin haihuwa, wannan ke raunana yanayin dubura.”

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.