Back to Africa Check

Yin sirace da albasa, tafarnuwa da lemon tsami ba zai kashe ƙwayar cutar Covid-19 ba

Wani bidiyo da aka rarraba a shafin Facebook sama da sau 4,200 na cewa yin sirace da tafasashen ruwan albasa, citta da tafarnuwa zai kashe cutar Covid-19.

A cikin bidiyo za’aga wata mace da kayan aiki ta kuma kira kanta da ma’aikaciyar jinya a sashen bada matsananciyar kulawa. Ta bawa jama’a shawarar su haɗa maganin da ta kira “ Covid tonic” ta hanyar tafasa albasa, lemon tsami, citta da tafarnuwa. Sannan a shaƙi tururin dahuwar haɗin sau uku a rana. 

“ Tururin yana da matukar zafi. Don haka idan da wata ƙwayar cuta a maƙogaro ko hanci zai kashe ta,” a cewar matar. 

Jita jitar cewa sirace na maganin ƙwayar cutar SARS-CoV1, ƙwayar cutar da ke jawo Covid-19 na ta yawa tun farkon yaɗuwar cutar a farkon 2020.

Africa Check ta ƙaryata makamantan wannan da’awar da dama. Tururi mai zafi baya maganin koronabairas a jiki- zai kuma iya yin lahani.

 

remedy_incorrect


Tururin ba zai isa ga ƙwayar cutar da ke cikin ƙwayar halitta ba

Wani  dan nazari da aka gudanar a watan Junairu 2021 ya tabbatar cewa shaƙar tururi na wani dumi zai rage yawan ƙwayoyin cutar da mutum ke fitarwa. Amma binciken sabo ne, ana buƙatar ƙarin bincike kafin a tabbatar da hakan. 

Abun la’akari shine binciken ya ce yin sirace ba zai kashe ƙwayar cuta ba, “ tururin, saman hanyoyin iska ya ke shiga kawai”. 

Likitoci da masana magunguna sun shaidawa Africa Check yin sirace baya maganin Covid-19.

Alberto Escherio, farfesa a fannin cututtakan annoba da abinci mai gina jiki na makarantar Havard fannin lafiyar jama’a a Amurka, ya ce “ ƙwayar cuta a jikin mutumin da ta harba tana shiga ƙwayoyin halitta, kuma sirace ba zai iya riskar su ba”.

Sirace zai iya jawo illa 

A watan Disembar 2020 masaniyar lafiya alumma Dr Arita Mosum ta shaidawa wata jaridar Afrika ta Kudu mai suna Mail & Guardian cewa sirace zai taimaka wajen buɗe hanci idan ya toshe amma baya maganin Covid-19.

“Wasu taimakon gidan da za’a yi zasu taimaka mutum yaji sauki, amma dai ba zamu ce ga maganin cutar Covid-19 ba a halin yanzu,” likitar ta ce. Sirace zai taimaka wajen buɗe hanci idan ya toshe amma ba maganin Covid-19 ba.” 

Shaƙar turiri mai mutukar zafi zai iya yin lahani.

Tsumoru Shintake, farfesa a cibiyar kimiyya da fasaha ta Okinawa da ke kasar Japan, ya taɓa gargadin Africa Check cewa ƙoƙarin sawa hancin zafi mai matukar yawa yana da hatsari zai iya kona mutum.

“Kar ku gwada shaƙar tururi. Zaku lahanta ƙwayoyin halitta na epithelium da ke hancin dan adam,” a cewar Shintake.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.