Back to Africa Check

Ana maganin dafin saran maciji mai dafi da ɓawon bishiyar kashu? Ba’a yi, a nemi kulawar likita

A taƙaice: Wani saƙon Facebook da ke yawo a Najeriya na iƙirarin cewa za’a iya maganin saran maciji ta hanyar tauna ɓawon bishiyar kashu. Wannan dai ƙarya ce, wanda maciji ya sara ya yi gaggawar neman taimakon likita.

A ƙalla mutane miliyan 2.7 macizai masu dafi ke sara a kowacce shekara. Tabbas 81,000 zuwa 138,000 daga ciki na rasa rayukansu, yayin da waɗanda suka rayu ke haɗuwa da wata naƙasa ta din-din-din

Yanki mai hamada na Afrika, yanki mai yawan ruwan sama na Asia, New Guinea, Tsakiya da Kudancin Amurka na daga cikin yankunan da suka fi gamuwa da saran macizai, inda aka fi sanin su da wuraren zafi masu fama da annobar- saran macizai

Wani saƙo da ke yawo a Facebook tun watan Satumba 2022, yayi iƙirarin cewa ɓawon bishiyar kashu na maganin saran maciji sosai. Saboda ruwan ɓawon na daidaita dafin saran macijin, saƙon ya ce.

An maimata da’awar a nan, nan da nan. Wannan rubutu ya ambaci wani bincike da akayi a shekarar 2009 a matsayin madogara. 

Shin cin ɓawon bishiyar kashu zaiyi maganin dafin saran maciji? Mun bincika. 

snake_venom_ false

Rigakafin dafi ce kawai maganin da aka sani da ke kiyaye mutuwa daga dafin saran maciji

Binciken 2009, sashen ilimin kimiyar halitta da ta sinadarai ta jami’ar Mysore da ke India ne suka gudanar da shi. A yayin binciken, anyi amfani da ɓerayen da aka saka musu dafin maciji mai dafi, sannan aka basu ruwan ɓawon kashu da aka haɗa a ɗakin gwaji.

Binciken ya nuna cewa ruwan ɓawon ya hana zubar jini, kumburi da ciwo a wajen saran macijin. Hatsarin da ke tattare da dafin na nan, sai dai ɓerayen da aka sakawa ruwan ɓawon basu yi saurin mutuwa ba.

Binciken ya tabbatar cewa ruwan ɓawon “taimakon-farko ne mai taimakawa saran maciji mai dafi”.

Sai dai kuma, maganin da ya fi aiki da dacewa don gujewa mutuwa bayan saran maciji mai dafi shi ne amfani da maganin da aka daɗe ana amfani da shi kuma yake aiki wato rigakafin dafi. Bincike da dama akan zafin saran maciji sun tabbatar da wannan, har da ma binciken 2009 da aka kawo a wannan rubutu. 

Zafin saran maciji ciwo ne da dafin da ke cikin saran maciji mai dafi ke haddasawa. Rigakafin dafi magani ne da ke tsayar da tasirin dafin. 

Farfesa Nicholas Casewell, darakta a cibiyar bincike da kawo agaji akan saran maciji da ke Biritaniya ya shaidawa Africa Check cewa zafin saran maciji abu ne da ke buƙatar taimakon gaggawa. Ya bada shawarar a yi gaggawar kai waɗanda maciji ya sara wajen jami’an kula da lafiya don basu rigakafin dafi. 

“Maganin saran macijin da kawai aka sani shi ne rigakafin dafi,” ya ce. 

Wasu hanyoyin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar akan kula da saran maciji, sun yi gargaɗi akan amfani da maganin gargajiya. Zasu iya jinkirta tasirin maganin asibiti, wanda hakan zai ƙara yin illa ba sauƙi ba.

Ɓawon bishiyar kashu ba rigakafin dafi ba ne, kuma ba zai kiyaye mutuwa ko naƙasa daga dafin saran macizai ba. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.