Back to Africa Check

Ba sai an kaucewa shan maganin hana ciwon jiki ba har na shekaru biyu bayan an yi allurar rigakafin Covid-19- tabbas kuma babu ‘hatsari’

Wata “sanarwa da akayi ga al’umma” wadda duka aka rubuta ta da manyan harufa na ta yawo a Facebook da WhatsApp, ta na cewa a “guji maganin ciwon jiki na diclofenac da sauran nau’ikan anasiziya wato magungunan hana jin zogin ciwo” na tsahon shekaru biyu bayan anyi allurar rigakafin Covid-19.

Sanarwar ta ce: “illolin allurar da waɗannan na kasancewa da hatsari”.

“Mahaifina (wanda masanin magunguna ne) ya ce wani likita ya hallaka matarsa cikin rashin sani bayan yayi mata allurar Diclofenac bayan dama ta yi allurar rigakafin Covid-19,” rubutun ya ƙara da cewa.

Kalmar anasiziya an ɗauko ta ne daga kalmar latin da ke nufin “rashin jin abu a jiki”. Anasiziya magunguna ne da ke hana jin zogin ciwo da rashin jin ɗadi, ana kuma amfani da su wajen sa mutum bacci, yayin da ake yi musu wani gwaji ko aikin tiyata.

A cewar hukumar lafiya ta Britaniya, diclofenac magani ne da ake amfani da shi wajen hana jin ciwo da zogi. Yana cikin rukunin magungunan da basu da siteroyid kuma suke hana kumburi, kamar asfirin, ibufirofen. Illolin da diclofenac ke iya jawowa sun haɗa da sa ƙuraje, ciwon ciki, jiri da tashin zuciya.

Shin zai zama hatsari amfani da anasiziya ko diclofenac a cikin shekaru biyu bayan anyi allurar rigakafin Covid-19?

vaccine announcement

Masana sun ce wannan da’awar ƙarya ce

Hukumar lafiya ta duniya ta ce daga cikin illolin da allurar rigakafin Covid-19 ke iya sawa sun haɗa da jin ciwo a wajen da akayi allurar, zazzaɓi, ciwon kai da ciwon jiki. Waɗannan kuma na nuna cewa jiki yana ƙoƙarin samar da kariya daga ƙwayar cutar.

Cibiyar yaƙi da cututtaka masu yaɗuwa ta Amurka ta ce za’a iya amfani da magunguna masara siteroyid masu hana kumburi wajen magance ciwukan da allurar rigakafin ka iya haddasawa. Amma an yi gargaɗin hana shan waɗannan magunguna yayin da za’a je yin allurar don gudun samun wasu ciwukan bayan anyi allurar. 

Edomwonyi Nosakhare, farfesa akan anasiziya a jami’ar Benin da ke jihar Edo a Najeriya, ya shaidawa Africa Check cewa da’awar ƙarya ce. Farfesan ya ƙara da cewa babu wasu dalilai a likitance da suka ce a kiyaye shan waɗannan magunguna bayan anyi allurar rigakafi. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.