Back to Africa Check

Ba’a sauya lokacin yin zaɓen 2023 ba, kamar yadda wata da’awa a kafafen sada zumunta ke iƙirari

“Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana ranar babban zaɓen 2023,” wani rubutu da akayi a watan Julin 2022 a wani guruf na Facebook a Najeriya, wanda ke da mabiya har sama da 280,000 ya fara da cewa

Hukumar zaɓe mai zamankanta (Inec) itace ke da alhakin gudanar da zaɓe a Najeriya. 

Rubutun na iƙirarin cewa za’a gudanar da babban zaɓen 2023 da za’a zaɓi shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, ƴan majalisar wakilai da ƴan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Fabrairu 2023. 

“Sannan za’a gudanar da na gwamnoni da ƴan majalisar jihohi  a ranar 4 ga watan Maris 2023,” rubutun ya ƙara da cewa. 

Mun ci karo da makamantan wannan da’awa a nan, nan da nan

Shin za’a gudanar da zaɓen Najeriya a wannan lokacin? Mun bincika. 

INEC_False

Babban zaɓen Najeriya zai kasance kamar yadda aka riga aka shirya

A ranar 26 ga watan Fabrairun 2022 Inec ta wallafa jadawalin lokaci da abubuwan da za’a gudanar a babban zaɓen 2023 a shafinta na yanar gizo. Wannan na ɗauke da kwanan watan manyan al’amuran da za’a gudanar da zasu kai ga zaɓen kansa. 

Bayanan da aka wallafa sun nuna cewa za’ayi zaɓen shugaban ƙasa dana majalisa (wakilai da ta dokoki) a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023. 

Zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni zai kasance a ranar 11 ga watan Maris.

Rubutun na Facebook bai bayyana lokaci ko dalilin da zai sa Inec ta sauya waɗannan muhimman lokuta a kalandar zaɓe ba.

Mun duba shafin Inec na yanar gizo da shafukanta na kafafen sada zumunta ko zamu ga wajen da ta ambaci sababbin lokutan zaɓen, bamu samu komai ba.

Irin wannan babban sauyi idan da gaske ne za’a samu manya gidajen jarida sun ruwaito. Bamu samu wata shaida da ta tabbatar da hakan ba. 

Irin waɗanna labaran ƙarya zasu iya saka masu kaɗa kuri’a ƙin zuwa su kaɗa kuri’a, su kuma shafi damar su ta shiga a dama a su a demokaraɗiya. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.