Back to Africa Check

Babban jami’in bankin cigaban Afrika bai nuna goyan bayan sa ga wani mai son zama shugaban ƙasa ba

Dimbin saƙonni a Facebook na iƙirarin cewa shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwunmi Adesina, ya nuna goyan bayan sa ga Bola Tinubu, ɗaya daga cikin dinbim ƴan siyasar da ke son su gaji kujerar shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023. 

Saƙonnin waɗanda aka wallafa su a watan Afrilun 2022, sun yi iƙirarin cewa Adesina ya ce: Matuƙar sanata Bola Ahmed Tinubu zai iya saka Legas ta zama ta 5 cikin garuwa masu yawan tattalin arziki a Afrika kuma jiha mafi tsaro a Najeriya, wannan ya tabbatar da abun da zai iya yi.”

Tinubu yayi gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya kuma cigaba da zama ɗan siyasa mai faɗa a ji a jihar da jami’iyyar All Progressive Congress

Bayan wata ganawa da Buhari a ranar 10 ga watan Junairun 2022, Tinubu ya bayyana aniyarsa ta son takarar kujerar shugaban cin Najeriya a zaɓen 2023. 

Amma Adesina, wanda yayi ministan noma a Najeriya daga shekarar 2011 zuwa 2015 ya goyi bayan tsayawar Tinubu takarar shugaban ƙasa? 

Adesina_Fake

Ofishin Adesina sun ƙaryata da’awar

An fara yaɗa da’awar a yanar gizo a watan Janairun 2022, jim kaɗan bayan Tinubu ya bayyana aniyarsa ta son yin takarar shugaban ƙasa.

Tun lokacin Adesina ya ƙaryata da’awar.

Jaridar Guardian ta ruwaito a ranar 12 ga watan Janairu cewa babban mai bawa Adesina shawara akan sadarwa Victor Oladokun ya ce da’awar “ƙarya ce, ɓarna ce kuma zamba ce”.

Oladokun ya ce Adesina bai nuna goyan bayansa ga kowa ba.

Sai dai kuma, magoya bayan Tinubu na cigaba da yaɗa da’awar a Facebook. Da’awar ƙarya ce.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.