Back to Africa Check

Babbar kotun duniya bata bawa Najeriya umarnin kada a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ba

A TAƘAICE: Za’a rantsar da Bola Tinubu a matsayin Shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu 2023, duk da cewa abokan hamayyarsa sun ƙalubalanci nasarar lashe zaɓe da yayi

Ana sa ran za’a rantsar da zaɓaɓɓan shugaban Najeriya Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu 2023, duk da cewa ana ta jayayya akan zaɓen. 

A ranar 1 ga watan Maris aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da akayi ranar 25 ga watan Fabrairu. Shi zai gaji Muhammadu Buhari, wanda mulkinsa ya taƙaita a karo na biyu, wanda kuma ya fara shi a shekarar 2015. 

Sai dai abokan hamayyar Tinubu na ƙalubalantar sakamakon a kotu. An fara saurarar ƙararrakin a ranar 8 ga watan Mayu.  

Ba’a sa ran za’a yanke hukunchi kafin a rantsar da shugaban ƙasar ba.

Wani rubutu a Facebook na iƙirarin cewa  kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya (ICC) ta buƙaci babban jojin Najeriya da ya tsayar da rantsarwar.

Rubutun na cewa: “Da ɗumi-ɗumi: Kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya (ICC) ta bawa babban jojin Najeriya umarnin ya dakatar da rantsar da Tinubu.”

Rubutun yayi ƙarin bayanin cewa: “Shugaban ICC ‘Greg Barclay’ ya bawa ‘Olukayode Ariwoola’ babban jojin Najeriya umarnin ya tsayar da rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, har sai kotu ta yanke makomar shugabancin ƙasar.” 

An samu irin wannan da’awar a Facebook a nan, nan, nan da nan

TinubuCourt_False

Mai magana da wayun ICC ya ce basu fitar da wani umarni ba

ICC na bincike, sannan idan ta kama suna shari’a da hukunta waɗanda suka aikata manyan laifuka a duniya. Waɗanda suka haɗa da laifukan yaƙi, kisan ƙare dangi da laifuka da suka shafi bil’adama. 

Mai shar’iah Olukayode Ariwoola shine babban mai shari’ar Najeriya, kuma mai kula da kotun ƙolin Najeriya. 

Rubutun na Facebook ya gaza banbance  hukumar wasan kiriket ta duniya, wadda itama ake mata laƙabi da ICC da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya. 

Barclay shi ne shugaban hukumar wasan kiriket, yayin da mai shari’ah Piotr Hofmański ya ke shugabantar kotun hukunta manya laifuka ta duniya

Mun bincika shafin kotun hukunta manya laifuka ta duniya na yanar gizo, Facebook da Tiwita ko zamu samu wani bayani da kotun ta wallafa akan hakan, amma bamu samu ba. 

Mai magana da yawun kotun, Fadl El Abdallah ya shaidawa Africa Check cewa hukumar bata fitar da wannan umarni ba. Ya ce: “ICC bata bada wani umarni makamancin wannan ba.”

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.