Back to Africa Check

Babu hujjar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa Omoyele Sowore ya ce ɗaliban jami’o’in Najeriya zasu samu kuɗi a hannun su duk zangon karatu, idan aka zaɓe shi

A TAƘAICE: A wasu maganganu da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ake sa ran ya zama shugaban ƙasa daga jam’iyyar African Action Congress ya yiwa ɗaliban jami’a alƙawarin zasu karɓi N100,000 a kowanne zangon karatu idan ya zama shugaban ƙasa. Babu dai hujjar da ta tabbatar Omoyele Sowore ya faɗi wani abu makamancin hakan.

 

Wani rubutun da ake yaɗawa a Facebook na cewa, ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya Omoyele Sowore yayi alƙawarin bawa ɗaliban jami’o’in Najeriya N100,000 kowanne zangon karatu US$230 idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Rubutun na ɗauke da hoton Sowore, kuma rubutun na cewa; “Ɗaliban jami’o’i na da ikon samun Naira dubu ɗari N100K a kowanne zangon karatu, idan an zaɓe ni”– AAC, Sowore.

Sowore ɗan takarar shugaban ƙasa ne daga jami’yyar Africa Action Congress AAC, a babban zaɓen ƙasar na shekarar 2023.

An fara yaƙin neman zaɓe a ranar 28 ga watan Satumba 2022, bisa tsarin Hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa.

Mun ci karo da wasu maganganun da aka danganta su ga Sowore a nan, nan da nan.

Shin Sowore yayi wannan alƙawarin? Mun bincika.

Sowore_False_2

Babu hujjar da ta tabbatar da maganar

Rubutun na Facebook bai bayyana lokaci da wajen da Sowore yayi maganar ba. Irin wannan rashin hujjoji alamu ne da ke nuna cewa da’awar da ke ta yawo a kafafen sada zumunta babu alamun gaskiya a tattare da ita.

Da muka duba sahihin shafin Sowore na Tiwita bamu ci karo da wannan maganar ba.

Babu kuma wani sahihin gidan jaridar da ya wallafa, wanda da ace maganar gaskiya ce dole ne gidajen jarida su wallafa.

A watan Yuni, Sowore yayi tsokaci mai tsaho akan yajin aikin malaman jami’o’in Najeriya a jerin saƙonnin da ya wallafa a sahihin shafinsa na Tiwita. Yayi kira ga ɗaliban Najeriya da su haɗa kansu, su kori wannan gwamnati abar ƙyama don KawoKarshenYajinaikinAsuuYanzu.

Amma dai bamu samu inda Sowore ya ce zai rabawa ɗaliban jami’a kuɗi ba bayan an zaɓe shi. 


 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.