Back to Africa Check

Babu hujjar cewa ganyen muliyan yana yaƙi da cutar asma ko wanke huhu

Kun san cewa ganyen muliyan na taimakawa wajen wanke huhu daga kwalta, yawu mai yauƙi da majina?” wani rubutu a akan wani hoto a wani saƙon Facebook ke tambaya. “Yana buɗe hanyoyin iska, yaƙar cutar asma da matsalolin huhu.”

Hoton na da taken “TSAFTACE HUHU”.

Muliyan, wani ganye ne da ya fito daga gidan nau’in ganyayyaki masu suna verbascum thapsus, ya samo asali daga Afrika ta arewa, Asia da Turai.

Wannan iƙirari akan cewa yana tsaftace huhu gaskiya ne? Mun bincika.
 

lung_cleanse_incorrect

Babu hujjar da ta tabbatar da da’awar 

Dr Richard Raine, likitan huhu a asibitin kula da masu lalurar numfashi a asibitin Groote Schuur da jami’ar Cape Town kuma ɗan ƙungiyar masana lafiyar ƙirji ta Afrika ta Kudu, ya ƙaryata da’awar.

Ya ce babu wata “hujja a yanzu a kimiyance” da ta tabbatar da hakan. 

Hanyar da tafi wajen zama cikin lafiyar huhu shi ne a “guji zama wajen da za’a iya shaƙar hayaƙin taba da sauran hayaƙi, shaƙe-shaƙe da kuma muhalli mai gurɓatacciyar iska”.

Asma ‘na da tsanani kuma zata iya zama barazana ga rayuwa’

A cewar asibitin Mayo, wata cibiyar ɗaukar karatun magunguna da ke Amurka, asma cuta ce da ke sa hanyoyin numfashi su ƙanƙance su kumbura, su kuma fitar da majina mai yawa. “Wannan na sa wahala wajen yin numfashi, ya sa tari, da fitar sauti yayin fitar da numfashi da kuma ɗaukewar numfashin.”

Matsalolin da suka danganci muhalli ko halitta ke jawo cutar.

Raine ya ce, asma cuta ce mai “tsanani kuma zata iya zama barazana ga rayuwa” wadda ke da magunguna a kimiyance, da manya masana kiwon lafiyar numfashi a duk faɗin duniya suka amince dasu”. Ganyen muliyan baya cikin magungunan. 

Magungunan da ake bayarwa na ƙara inganta rayuwa, su rage yawan zama a asibiti, su kuma kiyaye mutuwa daga cutar idan ta tsananata.”

Idan kuna fama da ciwon huhu kuje kuga likita, wanda zai duba ya gano matsalar ya bada maganin da ya dace.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.