Back to Africa Check

Babu hujjar cewa turara gaban ku yana da fa’ida a gare ku

Wani rubutu a Facebook na iƙirarin cewa “turaren yoni” na iya magance tabon jikin tsokar jiki, ƙaiƙayi da kuma fitar ruwan da ya saɓawa al’ada daga gaban mace.

“Yoni” kalma ce ta yaren Sanskrit da ke nufin al’aurar mace kuma yin wannan abun, wanda aka fi sani da turara gaban mace, na nufin mace ta tsuguna a saman kwanon tafasasshen ruwan maganin gargajiya.

Tabon jiki na iya samuwa a gaban mace bayan an ji ciwo, wanda hakan kan faru yayin haihuwa. Zai iya sa gaban mace ya ƙanƙance. Ƙaiƙayin gaba da kuma fitar ruwa wanda ba bisa al’ada ba ƙwayar cuta ke haddasa shi.

(A kula: Yayin da ake nufin “gaban mace” da al’aura gaba ɗaya, amma ana magana ne akan bututun da ke haɗa savis da bolba ko al’aurar ta da ake iya gani)

Mun zanta da masana magunguna don bincika ko turara gaban mace na sawaƙe waɗannan lalurori.

steaming_false

Babu hujja a kimiyance 

A cewar Makarantar magunguna ta Harvard da ke Amurka “babu wata hujja a kimiyance da ta goyi bayan turara gaba”.

Kwalejin mata da lalurar masu juna biyu ta Amurka, hukuma ce ta ƙwararru a Amurka ta shaidawa Africa Check cewa bata bada shawarar a turara gaba. Ta ce: “ Bama ma bada shawarar a yi wani abu a gaban haka kawai, hakan zai iya jawo matsala.”

Dr Tshi Nakanyane, wanda aka fi sani da Dr Naks, amintaccen likitan mata da masu lalurar juna biyu ne da ke aiki a asibitin Steve Biko Academic Hospital a Pretoria. Ya ce shima bai san wata hujja da ta goyi bayan wannan da’awar ba. 

“Turaren zai iya yin illa fiye da taimakawa. Zai iya ƙona ya kuma takurawa ma’aunin ph na gaban wanda zai iya ƙarawa gaban barazanar sake samun ƙwayar cuta,” Nakanyane yayi gargaɗi akai.

Hukumar Kimiyya ta Biritaniya bata bada shawarar a turara gaba don tsaftace shi ba. Ta bada shawarwari na kai tsaye ta yadda “gaban mace zai kasance cikin tsafta da lafiya”.

Ta ce: “Abu ne mai kyau a guji saka sabulai masu ƙanshi, jel ko maganin kashe ƙwayar cuta don zasu iya taɓa kwayar bakteriya mara illa da ma’aunin ph na gaban, su kuma hargitsa gaban. Ayi amfani da sabulun da bashi da ƙanshi don wanke kewayen gaban a hankali kullum. Gaban zai tsaftace kansa ta ciki da ruwan da gaban ke fitarwa na al’ada.”

A tuntuɓi likita idan an samu rauni a gaba, ƙaiƙayi ko fitar ruwa.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.