Back to Africa Check

Babu hujjar cewa ƴar takarar kujerar gwamna daga jam’iyyar Labour ta sha alwashin sai ta juyawa Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar baya

A TAƘAICE: An fara yaɗa jita-jita saboda ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar Labour Peter Obi bai haɗu da ƴar takarar gwamna Beatrice Itubo ba lokacin da ya kai ziyara jihar Rivers.. Amma ance Itubo bata da lafiya ne a lokacin, kuma babu hujjar cewa yanzu zata “tara ƴa’ƴan jam’iyyar” su juyawa Obi baya.

Wani saƙo da ke yawo a Facebook na iƙirarin cewa Beatrice Itubo, ƴar takarar gwamnan jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya daga jam’iyyar Labour, ta sha alwashin juyawa Obi baya, ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar. 

Najeriya na shirin gudanar da babban zaɓenta a farkon shekarar 2023. 

“Zan haɗa ƴa’ƴan jam’iyyar Labour a jihar su juyawa Peter Obi baya. -Comr Beatrice Itubo, ƴar takarar gwamnan jihar Rivers daga jam’iyyar Labour,” ɗaya daga cikin saƙonnin ke cewa. Ya kuma haɗa da hoton Itubo. 

Da’awar ta fito a wurare da dama a Facebook da Instagram. Ga wasu daga ciki a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan

An fara yaɗa da’awar ne bayan an zargi Obi, ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar shugaban ƙasa da ƙin ziyartar Itubo lokacin da yaje jihar Rivers. 

Gwamnan jihar Rivers mai ci a yanzu Nyesom Wike, wanda ɗan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne, shi ne ya gayyato Obi don ya ƙaddamar da sabuwar gadar Nkpolu-Oroworokwo a ranar 17 ga watan Nuwamba 2022. 

Masu suka sun soki Obi bisa rashin zuwan da yaƙi yi wajen Itubo, lokacin da ya je jihar Rivers. An ce Itubo bata da lafiya a lokacin. Obi ya bawa Itubo hakuri a wasu saƙonin Tiwita da ya wallafa, inda ya kira rashin zuwan nasa da “suɓucewa mara hujja” sannan kuma ya ce “ba’a sanar da shi rashin lafiyarta ba.”

LPObi_False.JPG

Zargin sayar da kujerar gwamna don samun kujerar shugaban ƙasa

An zargi Obi da sayar da kujerar gwamnan jihar daga jam’iyyar su don samun goyan bayan Wike akan takarar Obin ta shugabancin ƙasa. 

 Wike yayi kira ga Obi da ya sanar da magoya bayansa cewa jam’iyyar Labour ba zata samu nasara akan jam’iyyar PDP ba a zaɓen gwamna a jihar, ya kuma yi alƙawarin bawa yaƙin neman zaɓen Obi goyan baya. 

Obi ya karɓi tayin a zahiri, lokacin da ya ce: “Kai [Wike] ka san kai ne mai kula da komai. Ba zamuyi jayayya da kai ba; duk wanda yayi jayayya da kai bai san abun da ya ke yi ba. Ba zan ma fara ba. Ina roƙon, a bamu gwamnatin tarayya, mu kuma zamu baka jiha.”

Shin Itubo tayi iƙirarin zata saka ƴa’ƴan jam’iyyar juyawa Obi baya? 

Martanin da Itubo tayi bai yi dai-dai da da’awar da ake a nan ba

Saƙonnin babu wanda ya bada cikakken waje da lokacin da Itubo ta ce tana hamayya da Obi a jihar Rivers. Wannan rashin cikakken bayani alama ce da ke nuna kokonto. 

Gidajen jaridar Najeriya sun ruwaito abubuwan cigaba a kwanan nan da suka danganci takarar Obi, waɗanda suka haɗa da ban hakurin da yayi ga Itubo. Amma babu sahihin gidan jaridar da ya ruwaito cewa Itubo tana shirin yin hamayya da Obi. 

Da ta ke mai da martani a bainar jama’a, Itubo ta mai da da’awar da ke cewa Obi ya sayar da muradin ta na son yin takara, kuma ba zai bata goyan baya wajen zaɓe gwamna, abu mara muhimmanci

Wata sanarwa da Asim Adams, kakakin majalisar kula da yaƙin neman zaɓen Beatrice Itubo, ya fitar a shafin Itubo na Facebook a ranar 17 ga watan Nuwamba 2022, ya ce Obi yayi shaguɓe da kwatance yayin da yake mayarwa da Wike martani akan tayin da yayi masa. 

Abun takaicin shi ne, waɗannan shaguɓe da kwatance wasu sun ɗauke su sun basu fassarar cewa Mai girma Peter Gregory Obi ya yi watsi da aikin Beatrice Itubo da sauran ƴan takara a zaɓe mai zuwa  … wanda ya sha bambam da yadda abun ya ke,” sanarwa ta ce

“Ku kwantar da hankalin ku sani cewa, baya nufin sama da abun da ya faɗa, kamar yadda muka tabbatar daga tushe mai inganci da girma, inda aka ce kawai magana ce wadda bata wuce muhallin da akayi ta ba, wato don raha  … don haka a rangwanta duk wata ma’ana ta daban da za’a bata ko rashin fahimtar da za’ayi mata.”

Babu wata hujja a shafin Itubo na Tiwita cewa tana hamayya da Obi. 

Ta kuma sanar da ƴan jarida cewa maganar Obi, siyasa ce. Ta kuma ƙara da cewa “Obin da na sani hikimar sa tafi haka”. 

Da’awar bata tattare da wata hujjar da zata tabbatar da ita.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.