Back to Africa Check

Babu hujjar da ta tabbatar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa Tinubu ya ce ‘ya rasa duk abokan karatun sa a yaƙin Biafra’

A TAƘAICE: An addabi ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar APC Bola Tinubu da tambayoyi akan takardun sa na karatu. Sannan an kuma alaƙanta shi da wata magana mara hujja.

Wata magana mai ban mamaki da aka rarraba a Facebook an alaƙantata ga Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki a babban zaɓen Najeriya da za’ayi shekara mai zuwa. 

Maganar wadda aka haɗa ta da hoton Tinuba yana jawabi ga masu ɗaukar rahoto, na cewa: “Na rasa duk abokan karatu na a yaƙin Biafra”~~Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”

Bola Tinubu na takara ne daga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a zaɓen watan Fabrairun shekarar 2023. 

Yaƙin basasan Najeriya, wanda aka fi sani da yaƙin Najeriya na Biafra, an yi shi ne a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970. Yaƙin ya faru ne tsakanin wata jiha da ta ware kanta a kudu masu gabashin Najeriya da sunan jamhuriyar Biafra da gwamnatin tarayyar Najeriya, wanda ya jawo asarar rayukan mutane kimanin miliyan guda. 

An fara tambayoyi akan karatun Tinubu da takardun shaidar karatunsa tun shekarar 1999, lokacin da yayi takarar zama gwamnan jihar Legas. 

Takarar zama shugaban ƙasa da ya fito zai yi a shekara mai zuwa 2023, ya ƙara dawo da tambayoyin da aka yi a baya akan karatunsa, shekarunsa, shaidar shi waye, da kuma lafiyarsa

Festus Keyamo, kakakin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar APC, a wata tattaunawa da yayi a gidan talabijin yayi ƙoƙarin kawo ƙarshen waɗannan tambayoyi, amma dai da alamun hakan ya ci tura.

Irin wannan da’awar ta sake fitowa a Facebook a nan da nan

Shin Tinubu ya ce duk abokan karatunsa sun mutu a wajan yaƙin basasar Najeriya? Mun bincika.

TinubuQuote_False_2.png

Babu hujjar wannan maganar 

Rubutun na Facebook bai bada cikakken bayanin lokaci da wajen da aka ce Tinubu yayi maganar ba. Wannan dai-dai yake da ire-iren ƙarairayin da ake ƙirƙira a saƙonnin kafafen sada zumunta. 

Bincike a sahihin safin Tinubu na Tiwita da kuma shafinsa na yanar gizo, basu ba da hujjar da ta tabbatar da maganar ba. 

Babu kuma rahoton wannan maganar daga sahihan gidajen jaridar ƙasar, abu ne mai wuya ace ba’a fitar da rahoto akan hakan ba da ace yayi furucin. 

Babu wata hujja da ta nuna cewa Tinubu yace duk abokan karatunsa sun mutu a yaƙin basasar Najeriya. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.