Back to Africa Check

Babu hujjar da ta tabbatar cewa jam’iyya mai mulki a Najeriya APC na shirin hana ƴan arewa damar amfani da yanar gizo da rediyo, bayan da tsohon shugaban ƙasa ya marawa ɗan adawa baya

A TAƘAICE: Tsohon shugaban ƙasar Najeriya mai faɗa a aji Olusegun Obasanjo ya marawa Peter Obi baya a matsayin ɗan takarar sa a zaɓe mai zuwa. Yanzu kuma wasu kalamai na ƙarya sun yanke cewa jam’iyya mai mulki APC na son taƙaita amfani da ababen watsa labarai a wajen da suke da ƙarfi a arewa, don taƙaita cigaba da samun farin jinin Obi.

“Yanzu da ake ta tsayar da Obi a ko’ina, dole mu hana mutanen arewa samun damar amfani da yanar gizo ko rediyo,” abun da wani saƙo mai kama da wasu kalamai wanda ke yawo a Facebook ke cewa

An alaƙanta kalaman ga Festus Keyamo, mai magana da yawun cibiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki All Progressive Party (APC). 

Peter Obi shine ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar Labour a zaɓen ƙasar na 2023, wanda za’a fara a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya mai faɗa a ji Olusegun Obasanjo ya tsayar da Obi a matsayin ɗan takararsa a ranar 1 ga watan Janairu. 

Sauran ƴan siyasa ma an ruwaito cewa sun goyi bayan zaɓin Obasanjo. Tsayar da Obi, daga fitaccen mutum, ya jawo ce-ce-ku-ce daga sauran ƴan takarar shugaban ƙasa da magoya bayan su

Tasirin kalaman shi ne za’a samu rashin samun labarai a arewa, wanda ake ganin cewa babbar tunga ce ga APC, wadda zata taƙaita shaharar Obi a can saboda tsayar da shi a matsayin dan takarar da ake so, da akayi. Da’awar ta fito a Facebook a nan da nan

Shin da gaske Keyamo ya ce Obi zai taƙaita amfani da yanar gizo da rediyo a arewa bayan Obasanjo ya tsayar da shi a matsayin ɗan takararsa? 

Obi_KeyamoFalse

Babu hujjar da ta tabbatar da kalaman

Rubutun na Facebook bai bayyana waje da lokacin da Keyamo ya faɗi kalaman ba. Wannan na kama da irin labaran ƙaryar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta. 

Da muka binciki sahihin shafin Keyamo na Tiwita akan kalaman ba mu ga komai ba. 

Babu kuma wani sahihin gidan jaridar Najeriya da ya ruwaito labarin. Irin waɗannan kalamai masu jawo ce-ce-ku-ce akan hana masu zaɓe ƴancin su na siyasa, da zai kasance kanun labarai. 

Africa Check a kwanan nan ta tantance kalaman ƙarya da aka danganta su ga ƴan siyasa a nan, nan, nan, nan da nan


Yayin da zaɓen Najeriya ke ƙaratowa, ku guji faɗawa cikin bayanan ƙarya. Ku karanta hanyoyin da muka fitar na yadda zaku gane gaskiyar bayanai. Sannan nazarin mu ya taɓo bayanan ƙaryar da suke tashe a lokacin yaƙin neman zaɓe a Najeriya.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.