Back to Africa Check

Babu hujjar da ta tabbatar da cewa ɗan siyasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu yace ba zai halarchi muhawara akan shugabancin ƙasa ba saboda dalilin rashin lafiya

Wani rubutu da aka wallafa a Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa Bola Tinubu ya ce ba zai halarchi muhawara akan shugabancin ƙasa ba wadda gidan jaridan CNN International suka shirya, dalilin rashin lafiya. 

Tinubu shine ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya da za’ayi a shekarar 2023. 

Rubutun da aka buga a ranar 15 ga watan Yulin 2022 ya ce: “Bana jin daɗi, ba zan je muhawara akan shugabancin ƙasa ta CNN ba- Tinubu ya yi watsi da muhawara akan shugabancin ƙasa ta CNN. 

Mun ci karo da da’awowi makamantan wannan a Facebook a nan, nan da nan

Bola Tinubu ya faɗi hakan? Mun bincika. 

TinubuCNN_False

Babu shaidar yayi wannan magana

Rubutun na Facebook bai bayyana waje da lokacin da Tinubu ya furta wannan magana ba. 

Binciken da akayi a sahihin shafin Tinubu na kafar sada zumunta ta Twita da kuma shafinsa na yanar gizo ba a ga inda yayi wannan magana ba. 

Haka nan babu rahoton yayi wannan magana a sahihan gidajen jaridu na gida dana wajen ƙasar, wanda tilas a samu rahoto daga gidan jarida idan da ya faɗi hakan. 

CNN bata shirya muhawarar shugabancin ƙasar ba tun lokacin da suka fara aiki a ƙasar a shekarar 2016

CNN ta buɗe babban wajen gudanar da ayyuka a Legas, Najeriya a shekarar 2016, amma basu gudanar da muhawarar shugabancin ƙasar ba ga ƴan takarar shugabancin ƙasar ba har kawo lokacin haɗa wannan rubutu. 

Bincike a shafin CNN na yanar gizo da shafin su na Twita akan wannan muhawara bai sa anci karo da wani abu makamancin sa ba. 

Ana kuma gudanar da muhawarar zaɓe ne a cikin muhallin yaƙin neman zaɓen ne kamar yadda hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa ta tanada. A hukumance za’a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisa a ranar 28 ga watan Satumba 2022 zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu 2023.

Da a ce CNN ta shirya muhawarar shugabancin ƙasar Najeriya, da zai kasance kafafen yaɗa labarai na gida dana waje sun yaɗata matuƙa.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.