Back to Africa Check

Babu isassun hujjojin da suka tabbatar cewa soursop na maganin sankara

A TAƘAICE: Ba sai kun je da nisa ba a Facebook zaku ci karo da maganin ciwon sankara. Sai dai duk da cewa binciken ɗan itacen soursop da ke fitowa a wurare masu zafi, na nuna alamun nasara, amma babu binciken da ya isa a kira soursop da “maganin sankara, haka nan an hukunta wasu mutanen da ke nuna cewa hakan ne.

 

A watan Nuwamba 2022, wani guruf a Facebook mai sunan The Alkaline Momma suka buga wani bidiyo da yayi iƙirarin cewa soursop, wani ɗan itace da ke fitowa a wuri da ke da yanayin zafi, a kuma dazuzzukan wajen da ke yawan samun ruwan sama, wanda ke cikin rukunin ƴa’ƴan itacen fasadabur na iya magance cutar sankara. 

Taken da ke tare da bidiyon na tallata wani abu da aka yi da soursop mai tsada, wanda ake sayarwa a shafin kiwon lafiyar da ba ta asibiti ba. A ƙalla mutane 6000 suka kalli bidiyon. 

An yaɗa wasu saƙonnin da ke irin wannan iƙirarin a kafafen sada zumunta, galibi a sigar tallan abubuwan da ke ɗauke da soursop. Wani saƙon na Facebook ma cewa yayi ɗan itacen “yafi maganin sankara na kemotarafi karfi sau 1000”. 

Waɗannan da’awowi akan kiwon lafiya har sun sa wannan ɗan itacen samun guruf na kansa a Facebook, inda aka rarraba labaran yadda “irin binciken da akayi don samun hujjar da ta tabbatar da da’awar da ake akansa akan lafiya”. 

Waɗannan da’awowin sun samu bincike a kimiyance? Mun duba. 

Soursop_False.png

Binciken na nuna alamun tabbata … a kan ɓeraye da bututun yin gwaji

Soursop, wanda ake kira da gabiyola, ana samun sa a dazuzzuka masu yawan samun ruwan sama na wurare masu zafi a faɗin Afrika, Kudu maso gabashin Asia da Amruka ta Kudu. A maganin gargajiya, wasu sassa na itacen, da suka haɗa da ɗan itacen, ana amfani da su don maganin cutuka da dama. Wannan amfanin da ake da itacen ya jawo bincike akan yiwuwar samun abun da zaiyi amfani ga lafiya daga ɗan itacen.

Bincike da dama da akayi a akan abu mara rai, an duba tasirin ɗan itacen akan wasu tantanin halitta ko tsokar jiki, amma ba jikin ɗan adam ba. Ana kiran irin wannan bincike “binciken bututun gwaji”. Wasu binciken kuma sun binciki tasirin soursop a jikin ɓeraye da gafiyoyi. 

Wasu daga cikin waɗannan bincike sun nuna alamun tabbata. Binciken farko-farko sun nuna yiwuwar iya samun tasirin kiyaye kamuwa da cutar daga soursop akan sankarar ciki ta fankiriyas da ta mama. A kwanan nan, an bayyana yadda soursop ke rage yaɗuwar ƙwayoyin halittar cutar sankara. 

A shekarar 2021 nazarin sakamakon ɗinbim binciken da akayi sun tabbatar da cewa wasu abubuwan da ke jikin soursop zasu iya samar da abubuwan da zasu iya yin tasiri, da suka haɗa da ƙwayoyin halittar da zasu kiyaye tasirin cutar sankara. Amma dai kamar sauran binciken, waɗannan ma anyi su akan gafiyoyi, ɓeraye da wasu ƙwayoyin halittar jikin ɗan adam da aka keɓe. Masana ilimin kimiyya sau tari suna samun sakamako mabambanta, yayin da aka yi makamancin binciken akan ɗan adam, don haka ire-iren waɗannan bincike ana ganin su ne a matsayin binciken farko wanda bai kammala ba. 

Ba kasafai ake bincike akan ɗan adam ba. A wani bincike an taɓa tambayar masu fama da sankarar mama ko suna shan soursop da wasu saiwowi. Binciken ya samu dangantaka tsakanin shan soursop da raguwar tsahon rayuwa bayan ƴan wasu shekaru. Amma ba ya nufin soursop ne ya jawo raguwar tsahon rayuwa ba. Sai dai mu ringa tunawa cewa haɗuwar bincike ba ya zama dalilin samuwar hujja. 

Gargaɗi da hukuntawa akan da’awowin ƙarya akan soursop

Soursop bashi da wata illa wajen shan sa. “Babu ma yiwuwar cewa don an sha abu mai ɗauke da girabiyola zai yi wata illa,” a cewar wajen binciken sankara na UK

Amma likitoci sun yin gargaɗin shan zai iya jawo wata matsala ga wasu mutanen, kuma zai iya haɗuwa da magungunan hauwan jini da na wasu cututtukan. 

Saboda shaharar da yayi a matsayin magani ga mutane, sanannun cibiyoyin magunguna sun yi gargaɗi akan ɗan itacen. A shekarar 2017, hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka tayi gargaɗi ga kamfanoni 14 da ke iƙirarin ƙarya akan soursop da wasu hanyoyin maganin cutar sankara da ba na asibiti ba. 

Amintattun ƙungiyoyin cutar sankara sun musanta wannan da’awar, waɗanda suka haɗa da wajen binciken cutar sankara na UK, Cibiyar maganin cutar sankara ta Amurka da kuma ƙungiyar cutar sankara ta Afrika ta Kudu

Duk da cewa bincike akan gafiyoyi da cikin bututun bincike sun nuna alamun tabbatuwar da’awar, amma babu wata hujja da ta tabbatar soursop ko wani abu daga jikinsa na maganin cutar sankara a jikin mutane. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.