A TAƘAICE: Duk da cewa akwai mata da ke shekarun haihuwa kimanin miliyan 190 ke fama da cutar mahaifa ta indomitiriyosis a duk faɗin duniya, wannan haɗin ba magani ba ne. Ku nemi taimakon likita idan kun ji wasu daga cikin cututtukan da aka ambata a rubutun nan.
Zaku iya maganin indomitiriyosis a gida a cewar rubuce-rubucen da ke yawo a Facebook a Africa ta Kudu.
“Shin sakamakon gwajin da ku kayi ya nuna cewa indomitiriyosis ne ke hana ku samun juna biyu? Kuyi wannan haɗin a gida ku samawa kan ku lafiya da kanku.”
Indomitiriyosis cuta ce da tsoka makamanciyar tsokar da ke dai-daita mahaifa yayin al’ada ta ke fitowa a wajen mahaifa.
Mata masu wannan lalurar na samun wahala wajen ɗaukar juna biyu fiye da waɗanda basu da lalurar.
Rubutun na bawa masu karatu umarnin su sha haɗin itatuwa, gari da saiwowi daban-daban har kala shida sau biyu a rana.
“A saka duk kayan haɗi masu
gari a mazubi a wanke, a yanka duk ganyayyaki, a haɗa a cikin garin a saka 500ml na tafasasshen ruwa, a bar shi har tsahon mintuna 10”, rubutun ke cewa.
“Zaku iya yin haɗin da yawa a ajiye a na’uarar sanyaya abinci. A sha aƙalla na tsahon wata guda, zaku rabu da cutar indomitiriyosis.”
Irin wannan rubutun yayi ta yawo tun watan Disemba 2022, kuma an rarraba shi a guruf-guruf ɗin jama’a da dama masu dubban mabiya.
Africa Check ta taɓa tantance da’awa akan magungunan gida na ƙarya akan cututtukan da ke hana haihuwa, amma wannan dai-dai ya ke da waɗancan?
Mun bincika.

Indomitiriyosis cuta ce mai daɗewa a jiki kuma tana haddasa ciwo mai sauƙi da kuma mai tsanani
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ruwaito cewa a ƙalla mata miliyan 190 da ke shekarun haihuwa ke fama da lalurar indomitiriyosis a faɗin duniya.
Cutar na daɗewa a jiki, kuma zata iya saka ciwo mai sauƙi zuwa mai tsanani da ka iya saka zafi ko ciwo yayin da ake jinin al’ada, saduwar aure, yayin bayan gida da yayin bawali.
Indomitiriyosis na iya jawo tsananin ciwon mara, kumburin ciki, tashin zuciya, gajiya, rashin haihuwa, a wasu lokutan da cutar matsananciyar damuwa da ta fargaba.
Tunda wata tsoka ce ke fitowa ba dai-dai ba a wajen mahaifa, cutar indomitiriyosis sau tari na shafar wajen ajiyar ƙwan mahaifa, bututun ƙyanƙyasar ƙwan da kuma tsokar da ke jikin ƙugun mace. Sannan a wasu lokutan tsokar zata iya fitowa a wasu sassan jiki kamar huhu.
Ba’a san takamaimai me ke haddasa cutar ba, amma akwai maganganu da dama akan musabbabin cutar kamar gado da matsalar garkuwar jiki.
Ba’a magance cutar sai dai ayi maganin alamun cutar
Maganin cutar ya danganta ga yadda alamun cutar suka tsananta a jiki, shekaru da kuma yadda aka shirya ɗaukar juna biyu, cewar asibitin Cleveland, wato wata cibiyar lafiya a Amurka.
Wasu daga cikin magungunan sun haɗa mda magungunan da zasu dai-daita ƙwayoyin halittar jiki da tsokar jiki don takurawa cutar, waɗanda suka haɗa da maganin tsarin iyali, maganin kashe raɗaɗi da kuma tiyata.
Sannan ana yin tiyata a wasu lokutan, haka nan likitoci na iya buƙatar a cire mahaifa gaba ɗaya don sawwaƙe matsanantan alamomin ciwon. Cire mahaifa na nufin cireta ta hanyar yin tiyata, wanda hakan kuma zai sa mace ba zata ƙara yin jinin al’ada ba kuma ba zata ƙara ɗaukar juna biyu ba.
Bincike da dama sun nuna cewa ko da anyi tiyata ba lalle ne hakan ya magance duka alamonin cutar ba, sauye-sauyen da suka danganci cutar zasu iya bullowa ko da bayan anyi tiyata ne.
A halin yanzu dai babu maganin cutar mahaifa ta indomitiriyosis har da maganin da aka saka a wannan rubutu. Waɗannan rubuce-rubuce zasu iya jefe matan da ke fama da lalurar tunanin za su samu sauƙi, su kuma hana matan zuwa asibiti don ganin likita.
Africa Check bata samu wata madogara ba akan yiwuwar ko waɗannan magunguna na magani ko warkar da cutar.
Akwai abubuwan da za’a iyayi a gida don ganin an samu sauƙin alamomin cutar. Sun haɗa da saka jakar ɗumama jiki a ƙasan mara, yin wanka da ruwan ɗumi da kuma keɓe wasu mintuna a kowacce rana don a huta.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment