Back to Africa Check

Ɓawon bishiyar ɗorawa na maganin hawan jini

Wani rubutu a wani shafin Facebook mallakin yan Najeriya “ Solarababa herbs” yayi iƙirarin cewa ɓawon bishiyar ɗorawa zai “ kashe hawan jini”.

Rubutun ya bayyana yadda za’a haɗa maganin. “ A tafasa maganin da ruwa. A sha adadin (5ml) kullum har tsahon makwanni biyu.”

Amma wannan zaiyi maganin hawan jini? Mun bincika.

herbs

A je a ga likita don samun kulawar da ta dace

Ɗorawa wadda aka fi sani da bishiyar kalwa, bishiya ce da ke da amfani da dama kuma ake samun ta a ƙasashen Afrika da dama.

Cutar hawan jini ko hauhawar jini, cuta ce mai matsanani ga kiwon lafiya, cutar na sa jini ya hau. Tana kuma zama barazana ga lafiyar ƙoda da zuciya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yankin Afrika ne ke da mafi yawan masu fama da cutar a duniya- kashi 27% na daga cikin mutane biliyon 1.13 da ke fama da cutar.

Mun tuntuɓi Jacob Awobusuyi, Farfesa a fannin kiwon lafiya na jami’ar jihar Lagos don ya tofa albarkacin bakinsa akan wannan rubutu na Facebook.

“Bani da masaniya ko wani bayani akan hakan, ya ce. “ Maganin hawan jini ya fi ƙarfin a ce asha magani kawai. Akwai abubuwa da dama da ake don a shawo kan cutar.”

Awobusuyi ya ce masu fama da cutar hawan jini su je su ga likita don a basu kulawar da ta dace.

Hukumar kiyaye yaɗuwar cututtuka ta Amurka, ta ce ta hanyar zuwa duba jini akai akai ne kawai za’a gano idan mutum na ɗauke da cutar. Daga cikin hanyoyin da za’ a kiyaye kamuwa da cutar hawan jini sun haɗa da cin abinci mai lafiya, rage ƙiba, motsa jiki, rage shan barasa da samun isasshen bacci. 

Africa Check ta tantance da’awa makamanciyar wannan da ke cewa garin abokado na maganin hawan jini da wasu cututtuka.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.