Back to Africa Check

Bekin soda bata kashe ƙwayar cuta da ƙwayoyin halittar cutar sankara ba

“HET JY GEWEET? … KOEKSODA MAAK VIRUSE IN JOU LIGGAAM DOOD. VAN KANKER SELLE - TOT WAT OOK AL WIL BROEI.”

Wannan wata da’awa ce a yaran Afrikaans dake ƙunshe cikin wani rubutu a Facebook. Da’awar na nufin: Kun san cewa? Bekin soda na kashe ƙwayoyin cuta a jikin ku. Kama daga ƙwayoyin halittar cutar sankara- zuwa duk wani abu da zai haifar.” 

Bekin soda ko bikarbonat soda sinadarin alkali ne da ake amfani da shi wajen sa abincin da ake da filawa  ya tashi don yayi kyan gashi.

Saƙon na cewa a zuba ƙaramin cokali ɗaya na bekin soda ko sama da haka a milimita 500 na ruwa a sha.

“Al wat Bicarbonate of Soda doen is plaas suurstof in jou liggaam en balanseer jou liggaam se pH levels,” saƙon ya cigaba da cewa. Wanda ke nufin: “Duk bikarbonat na Soda na saka oksijin a jikin ku, ya kuma daidaita muku pH na jiki.”

Ya kuma ƙara da cewa da rands ƙalilan zaku iya kare jikin ku, ku kuma kiyaye kanku daga ƙwayoyin cututtuka masu hatsari. Rand dai shine kudin da ake amfani da shi a Afrika ta Kudu. 

Shin hakan gaskiya ne? Shan bekin soda da aka haɗa da ruwa na kashe ƙwayoyin cuta da ƙwayoyin halittar cutar sankara?

sodahealth

Shirme’- Ƙwararriya akan ƙwayoyin cuta 

“Wannan shirme ne,” cewar Farfesa Diana Hardie, ƙwararriyar likita akan ƙwayoyin cuta kuma shugabar ɗakin binciken ƙwayoyin cuta na asibitin Groote Schuur da ke Afrika ta Kudu.

“Yayin da oksijin ta kasance abu mai matuƙar muhimmancin wajen kasancewar mu da rai, sai dai bata kashe ƙwayoyin cuta.” Sannan abun da kawai ke kawo mana oksijin a jiki shine huhu”, ta shaida mana- ta kuma ƙara da cewa ba dai bekin soda ba. 

“Jiki na fitar da ƙwayoyin cuta ta hanyar garkuwar jikin wanda ya kamu da ƙwayar cutar,” Hardie ta ce. 

“Da zarar an samu martani daga garkuwar jiki, sinadarin garkuwar jiki wato antibodis da T limfosayat zasu kawar da ƙwayoyin halittar da suka kamu da cutar da ƙwayoyin halittar cutar. Alluran rigakafi na assasawa jiki samar da garkuwa daga cuta.

Duk da cewa “akwai magungunan da ke hana ƙwayar cuta sake fitowa” kamar magungunan antibairal da ake amfani da su ga masu cutar HIV, sai dai mafi akasari ana barin tsarin garkuwa a jiki yayi wannan aikin.

Shirme- a cewar ƙwararriya akan cutar sankara

Wannan ai shirme ne,” a cewar Farfesa Janet Poole, shugabar sashen kula da ciwukan da suka shafi jini da cutar sankara ga ƙananan yara na asibitin karatu na Charlotte Maxeke da ke Johannesburg a Afrika ta Kudu. Unkoloji na nufin masana akan cutar sankara. 

“Da zarar ka kamu da ƙwayoyin halittar cutar sankara ba zaka iya kawar da su da komai ba da ya wuce maganin asibiti,” Farfesan ta shaida mana. Waɗanda suka haɗa da kimotarafi wato magani da magunguna, radiyeshan wato magani da ta hanyar abu ya ratsa jiki, immunotarafi wato bunƙasa garkuwar jiki don tayi yaƙi da cutar ko kuma maganin irin nau’in ƙwayar cutar sankarar da ta kama mutum”.

Sankara na nufin cututtaka da dama waɗanda tantanin ƙwayar halitta ke fitowa fiye da na al’ada, wanda yake yaɗuwa ya kuma hallaka tsokar jiki.

Duk da cewa a wasu lokutan ƙwayoyin cuta na haddasa cutar sankara, basu kaɗai ke jawo ta ba. Abubuwa da dama na haddasa ta. 

Asibitin Mayo, wani asibitin a Amurka ya ce, don rage hatsarin kamuwa da cutar sankara, a guji shan sigari, a guji shiga matsananciyar rana, a ci abinci mai kyau da gina jiki, a ringa motsa jiki, a daina yawan shan barasa, a kuma ringa ganin likita don duba ko mutum na ɗauke da cutar, a kuma ringa yin alluran rigakafin da suka dace. 

Africa Check ta taɓa tantance wata tsohuwar almara da ke cewa wai rashin daidaiton ma’aunin pH na jiki ke jawo sankara.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.