Back to Africa Check

Bidiyon da aka sauyawa kamanni na iƙirarin ƙaryar cewa wani likita ɗan Najeriya ya ‘ƙirƙiri’ maganin da zai warkar da cutar hawan jini

A TAƘAICE: Wani bidiyo da aka saka a Facebook aka kuma kalle shi sau da dama yayi iƙirarin cewa wani likita ɗan Najeriya ya samu maganin warkar da cutar hawan jini. Ana gargaɗin ku da ku kiyayi bidiyon- bidiyon an sauya shi, kuma abun da ya ke faɗa ƙarya ce.

Wani likita ɗan Najeriya ya samo maganin “warkar” da cutar hawan jini har abada, ko mu ce abun da wani bidiyo da aka saka a Facebook a watan Nuwamba 2023 ke cewa. 

Bidiyon yayi kama da labarai wanda mai gabatar da shirye-shirye Kayode Okikiolu na gidan talabijin na Channels, wani shahararren gidan yaɗa labarai a Najeriya ke gabatarwa. 

Taken da ke ƙasan akwatun talabijin na cewa “bincike mai ban al'ajabi”. Mai bada labaran na cewa, maganin na daidaita bugun jini a kwanaki uku. 

Ya kuma ce: “Ta amfani da maganin sau ɗaya jiki zai warke kwata-kwata, za’a kuma manta da cutar har abada.” 

Bidiyon ya kuma nuna masu kallo su na sauraran wani da ba’a san ko waye ba, wata kila dai shine likitan da ke faɗar amfanin maganin, waɗanda ya ce sun haɗa da rage barazanar samun shanyewar jiki ko ciwon zuciya. 

Bidiyon ya cigaba da iƙirarin cewa ƴan Najeriya tuni sun fara gwada maganin, don haka ya ke kira ga jama’a da su biyo “yaƙin neman”. An kalli bidiyon sau 33,000. 

An saka bidiyon a Facebook a nan, nan, nan da nan

Da gaske akwai magani irin wannan? Mun bincika. 

/HypertensionCure_False

Menene hawan jini

Ana kuma kiran ciwon da hauhawar jini. Hawa ko tashin bugun jini cuta ce babba wadda jini ke takurawa jikin hanyoyin jini. Wanda hakan ke sa zuciya ta ringa aiki da tura jini ga sassan jiki fiye da yadda ya kamata tayi. 

Kasancewar mutum ɗauke da cutar hawan jini na ƙarawa mutum damar samun lalurorin zuciya, ƙwaƙwalwa, ƙoda da sauran cututtuka, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya. Hukumar ta ƙimasta cewa namiji ɗaya cikin maza huɗu da mace ɗaya cikin mata biyar- kimanin mutane biliyan ɗaya- na ɗauke da cutar, wadda tana ɗaya daga cikin cutukan da ke saurin kisa. 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, yankin Afrika na da mafi yawan masu cutar hawan jini, wato kashi 27% na al’umma. Haka nan kuma kusan rabin masu manyan shekaru, wato kashi 46% basu san suna ɗauke da cutar ba. A Najeriya, an ƙimanta cewa manya miliyan 19.1 da ke tsakanin shekaru 30 zuwa 79 na ɗauke da cutar, a bayanan hukumar na kwanan nan. 

Alamu sun nuna an sarrafa bidiyon ne

Idan aka kalla a tsanake, bidiyon na da wasu ayoyin tambaya. Motsin leɓen bai yi dai-dai da sautin muryar da ke cikin bidiyon ba. Laɓɓan sa na motsi dai-dai har ƙarshen bidiyon, wanda hakan bai kamata ya kasance ba tunda kowacce kalma da yadda ake furta ta. Wannan na nuna cewa an sarrafa bidiyon yadda ake so. 

Bidiyon kuma bai bada cikakken bayanin maganin ko wanda ya ƙirƙire shi ba, bai ma ambaci sunan wanda ya ƙirƙira ba. 

Binciken shafin yanar gizo na Channels da tashar su ta YouTube bai sa an samu bidiyon ba. Ganin yadda ciwon hawan jini ya addabi duniya, ya kamata ace an bada rahoton samuwar maganin waraka a duk duniya. 

Bidiyon yayi amfani da kalamai masu motsa rai, kamar cewa maganin “bincike mai ban al’ajabi”, sannan kuma da kira ga mutane da su shiga yaƙin neman da basu san ko na me ba, wanda “zai ƙare a yau”. Amfani da gaggawa abu ne da aka san masu labaran ƙarya nayi. 

Ƙungiyar masu ciwon zuciya ta Amurka ta ce ba za’a iya warkar da hawan jini ba, amma za’a iya rayuwa da shi ta hanyar sauya yadda ake gudanar da al’amuran rayuwa, idan ta kama kuma ana haɗawa da magani. 

Abubawa kamar wannan bidiyon zasu iya sa masu fama da matsanancin ciwon daina shan maganin asibiti, hakan kuma hatsari ne ga rayuwarsu. Mutane zasu kuma iya faɗawa tarkon ƴan damfara, su kuma yi asarar kuɗaɗen su. 

Ku koyi yadda zaku gane bidiyon bogi da na ƙarya ta hanyar karanta hanyoyin a nan

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.