Back to Africa Check

Bidiyon da ba shi da ƙwanan wata bai nuna ƴan bindiga na jira akan titin Abuja-Kaduna bayan kai hari kan jirgin ƙasa a watan Maris 2022

Wani bidiyo da aka saka a Facebook Najeriya a watan Afrilu 2022 na nuna gungun maza, waɗanda ke ɗauke da bindigogi akan titi a karkara. Da farko an nuno su suna ta yawo a wajen, suna maganganu, sai kuma aka ji waƙa ta fara tashi har aka ga suna rawa. 

“WANNAN ƘASA TA TASHI DAGA AIKI,” taken da ke tare da bidiyon waɗanda aka rubuta su da manyan harufa ke cewa. “ƳAN FASHIN DAJI SUN TOSHE TITIN ABUJA ZUWA KADUNA SUNA JIRAN ABABEN HAWAN DA ZASU YI GARKUWA DA SU.”

An kalli bidiyon sama da sau miliyan 1.4, mutane 6,700 sun yi tsokaci akan bidiyon, yayin da aka kuma rarraba bidiyon sau dubu 25,000.

Titin Abuja zuwa Kaduna, titi ne da ke tsakiyar ƙasar kuma ya ke haɗa babban birnin tarayyar Najeriya da garin Kaduna, wanda gari ne mai muhimmanci a arewacin Najeriya. Titin ya shahara da hare-hare wanda ya haɗa da garkuwa da mutane. 

An saka bidiyon ne bayan harin da ƴan bindiga suka kaiwa jirgin ƙasa a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja ranar 28 ga watan Maris. Inda aƙalla mutane 8 suka rasa rayukansu. Yayin da mutane 168 ake zargin an yi garkuwa da su ko sun ɓace. 

Amma shin bidiyon mai tada hankali, ya nuno ƴan fashin daji akan titin Abuja zuwa Kaduna a watan Afrilu suna jiran ƙarin mutanen da zasuyi garkuwa dasu? 

Kaduna_express

‘Bidiyon dai bashi da kwanan wata’ an fitar da shi a watan Janairun 2022

Ciyayi masu haske, harshen da mazan ke magana da shi da waƙar da aka ji a cikin bidiyon duk na nuna alamun an ɗauki bidiyon a arewacin Najeriya. 

Sai dai titin layi ɗaya ne wanda babu wata alama akan sa. Yayin da titin Abuja zuwa Kaduna tituna ne guda biyu, kowanne titi kuma an masa alama a bayyane. 

Mun kuma gano cewa bidiyon ya shafe aƙalla watanni huɗu a yanar gizo- idan ma bai fi haka ba. Tashar YouTube ta Sahara ta ɗora bidiyon a watan Janairu da taken ‘bidiyo mara kwanan wata na wasu gungun ƴan fashin daji da suka haɗa da sojoji yara suna rawa”.

Bidiyon ya fito a yanar gizo tun kafin a kai mummunan harin da aka kaiwa jirgin ƙasa a watan Maris.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.