Back to Africa Check

Buhari bai cewa sojojin Najeriya suyi shirin yaƙi ba

Wani hoto da ke yawo a Facebook na nuna shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari yana cewa sojojin ƙasar da su “yi shirin yaƙi”.

Hoton na yanayi da hoton da ake ɗauka na hoton allon waya wato sikirinshot na wani rubutun tiwita daga shafin @MBuhari, wanda shafi ne mallakin Buhari

Rubutun tiwitan na cewa: “Muna tare da Ukraine a wannan mawuyacin hali, bayan magana da shugaba Biden akan irin tsare-tsarensa, na sanar da jami’an sojojina da suyi shirin yaƙi! Ba zamu bar wannan ya kuɓuce ba.”

A ranar 24 ga watan Fabrairu ne ƙasar Rasha ta mamaye maƙwabciyarta, ƙasar Ukraine, a lokacin kuma mummunan faɗan da ya ɓarke tsakanin su ya zama kanun labaran da aka fi yaɗawa a duk faɗin duniya.

Shin da gaske Buhari yayi wannan rubutun a shafinsa na tiwita, wato cewar, ya sa sojojin ƙasar cikin shirin ko ta kwana, bayan ya zanta da shugaban ƙasar Amurka Joe Biden? Mun bincika.

Buhari_Military

Babu hujjar da ta tabbatar da sanarwar

A sahihin shafin Buhari na tiwita rubutu na ƙarshe da akayi an yi shi ne a ranar 1 ga watan Yunin 2021, kwanaki kaɗan kafin gwamnatin tarayya ta haramta amfani da shafin tiwita a ƙasar.

An ɗage haramcin amfani da shafin a ranar 12 ga watan Janairu 2022, amma shugaban ƙasar baiyi rubutu a shafin sa ba bayan ɗagewar.

Wata alamar da ta nuna cewa hoton allon wayar na bogi ne, shi ne yawan kurakuren da ke cikin rubutu, wanda abu ne mawuyaci ace daga ofishin shugaban ƙasa saƙon ya fito.

Babu kuma wata kafar yaɗa labarai a Najeriya da ta fitar da labarin. Duk hujjoji sun tabbatar da cewa ƙirƙirar labarin akayi.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.