Back to Africa Check

Cutar Covid-19 ba sabuwar nau'in cutar zazzaɓin cizon sauro ba ce, dole ana buƙatar ayi rigakafin kamuwa da cutar

Covid-19 bata da banbanci da cutar zazzaɓin cizon sauro don za'a iya magance ta da shan magungunan cutar zazzaɓin cizon sauro, don haka ba'a buƙatar rigakafin Covid-19 a Afrika, a cewar wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook mallakar” Radio Biafra London” a Junairun 2021.

“ Afrika bata buƙatar rigakafin Covid-19,” a cewar saƙon. “ Cutar Covid-19 bata da banbanci da cutar zazzaɓin cizon sauro. Cutar sauyi ne aka yiwa ƙwayar cutar zazzaɓin cizon sauro a ɗakin gwaje-gwaje. Ƙwayoyin halittar da ke samar da cutar iri daya ne. Kada wanda ya kuskura ya kawo mana rigakafi a matsayin bashi. Magungunan zazzazaɓin cizon sauro zasu iya yi mana maganin cutar Covid-19. Kada a kuskura, na nanata kada a kuskura.”

Sai dai fa wannan batu ƙarya ce tsagwaranta. Binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar cutar zazzaɓin cizon sauro da Covid-19 basu da alaka da juna.

 

Covid-19 not malaria

 

Ƙwayar cutar da aka fi sani da farasayit ke jawo zazzaɓin cizon sauro, yayin da ƙwayar cutar bairas ke jawo cutar Covid-19

Ƙwayar cutar filasmodiyom farasait ke jawo zazzaɓin cizon sauro, yayi da ƙwayar cutar bairas ke jawo cutar Covid-19, Adamu Bakare Farfesa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a arewacin Najeriya ya shaidawa Africa Check hakan. Cutar Covid-19 sabuwar ƙwayar cutar Koronbairas da aka sani da Sars CoV-2 ke jawo ta.

“ Wasu daga cikin alamomin cutar Covid-19 na kama da alamomin zazzaɓin cizon sauro, amma dai sam basu da alaka da juna,”a cewar Bakare.

“ Filasmodiyam ya fi Koronabairas girma nesa ba kusa ba. Za'a iya ganin ƙwayar cutar Filasmodiyam a madubin duba ƙwayoyin cututtuka na yau da kullum amma ƙwayar cutar bairas sai a madubi na musamman ake iya ganinta. Don haka musabbabin su ba ɗaya ba ne, musabbabin Covid-19 da zazzaɓin cizon sauro daban daban ne.”

Magungunan cutar zazzaɓin cizon sauro basa maganin cutar Covid-19

Farfesa Olugbenga Awobusuyi shugaban sashen kula da ƙoda na Kwalejin koyan aikin likitanci ta jami'ar jihar Lagos, ya shaida mana cewa yin allurar rigakafi zaiyi maganin daukar cutar Covid-19 yayin da maganin zazzaɓin cizon sauro ba zai kiyaye mutum daga kamuwa da zazzaɓin cizon sauron ba. 

“ Zazzaɓin cizon sauro ƙwayar cutar Farasayit ke jawo ta, yayin da cutar Covid-19 ƙwayar cutar bairas ke jawo ta,” Farfesan ya ce. “ Ana ta cewa wasu magungunan cutar zazzaɓin cizon sauro kamar Hydroxychloroquine suna da tasiri wajen magance cutar Covid-19. Babu wani bincike a kimiyance da ya tabbatar da hakan. Rigakafi itace mafi a'ala. Ina bawa jama'a shawarar su rungume ta duk sanda ta iso nan Najeriya.”

A watan Yunin 2020, Hukumar Lafiya ta Duniya ta watsar da gwajin maganin Hydroxychloroquine a matsayin maganin cutar Covid-19.

Hukumar lafiya ta Duniya tace tayi hakan ne bayan tayi nazarin hujjojin da suka tabbatar da cewa Hydroxychloroquine baya rage adadin waɗanda ake ƙwantarwa a asibiti su kuma mutu sanadiyar Covid-19. 

Ƙwararru a fannin kiwo lafiya da muka tuntuɓa suna kira ga jama'a da su dauki matakan kariya, saka tankunkumin rufe fuska, bada tazara tsakanin juna, wanke hannaye akai akai da kuma zuwa asibiti da zarar an ji alamun cutar, a guji sha magunguna ba tare da izinin likita ba.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.