Back to Africa Check

Ɗan damfara kuma ɗan asalin Najeriya da ke tsare Hushpuppi bai sake yin damfarar $400, 000 ba

Wasu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da suka watsu na iƙirarin cewa ɗan damfara kuma ɗan asalin Najeriya da ake zargi yayi wata damfarar, ta dalar Amurka $400, 000 yayin da yake Amurka. 

Wannan labarin ya fito a jaridu da dama da shafukan bada labarai na yanar gizo wato blogs

Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya kuma shahara da nuna rayuwarsa a shafin sada zumunta na Instagram. An cafke shi a watan Yunin 2020 a garin Dubai. Mahukuntan Amurka sun bayyana cewa yayi laifukan da suka sa waɗanda suka faɗa tarkonsa asarar kuɗi kusan dalar Amurka miliyan $24. 

Abbas na fuskantar tuhuma akan laifukan damfara akan yanar gizo da kuma satar kuɗade, ana tuhumar tasa ne a wata kotun gunduma ta Amurka a gundumar tsakiya a California. Ya dai amsa laifukan da ake tuhumarsa, za’a kuma hukunta shi a watan Yulin 2022

Da’awar tayi ƙwatanƙwacin wata takardar shaidar rantsuwa da Andrew John Innocenti wani jami’i na musamman na hukumar bincike na musamman ta Amurka ya gabatar a kotu a ranar 16 ga watan Maris 2022. 

Shin Hushpuppi ya sake yin damfarar dala $400,000 a tsare a gidan yarin Amurka? Mun bincika. 

Hushpuppi_Scam

An yi amfani da katin biyan kuɗi da ake amfani da shi a Amurka don bada tallafi wajen damfarar

Takardar shaidar rantsuwar na cewa Abbas tare da wani sun damfari gwamnatin Amurka wajen karɓar tallafin Covid ta hanyar anfani da katin biyan tallafin kuɗi na (EIP). 

Katin cire kuɗin dai ana bawa yan ƙasar Amurkan da suka cancanta. Katin na ɗauke da kuɗi biyan farko ƙarƙashin tallafin Koronabairas, don taimako kuma yana cikin dokar kiyaye tattalin arziki ta gwamnatin Amurka. Ana kuma amfani da katin wajen biyan kuɗaden tallafin harajin da ya danganci Covid ƙarƙashin dokar 2020 da kuma dokar agaji ta Amurka ta shekarar 2021

Takardar shaidar rantsuwar ta ce, Abbas na samun damar buga waya da dama ba tare da an hana shi ba, haka nan ya samu damar amfani da yanar gizo a gidan yari. Ta kuma ce yana gidan yarin ya sayo katunan 58 EIP, waɗanda da su yayi amfani wajen kwasar kuɗin. 

‘ Bogi ne’ - a cewar ƙwararre akan amfani da kimiyya wajen binciken na’ura mai ƙwaƙwalwa

Takardar shaidar rantsuwar ta bogi ce, a cewar Gary Warner, daraktan cibiyar amfani da kimiyya wajen binciken na’ura mai ƙwaƙwalwa ta jami’ar Alabama dake Birmingham a ƙasar Amurka.

“Jama’a na tambaya ta ko da gaske ne #Hushpuppi ya samu kuɗaɗen haramun ta amfani da katin #kuɗaɗen haraji yana gidan yari. Takardun da suka nuna an sauya su ne, sun kasance takardun rantsuwa ne da aka yi a watan Yunin 2020 aka sauya,” Warner ya wallafa a shafin sa na Twita a ranar 17 ga watan Maris 2022. 

“Sabuwar damfarar, ƙarya ce, an ƙirƙire ta ne don jama’a su samu shiga shafin EIP na yan damfara.”

Wani link da ke jikin takardar rantsuwar zai kai mutum wani shafi da ke tayin katunan EIP masu ɗauke da kuɗaɗe daga dala $1,400 zuwa dala $8,400. Shafin na bukatar baƙin da suka shiga shafin da suyi rijista kafin shiga.

Wannan yayi kama da wata da’awa da Africa Check ta tantance a watan Nuwambar 2020.

Farfesa Boniface Alese ƙwararre akan tsaro a yanar gizo kuma malami a jami’ar fasaha ta tarayya da ke Akure a Kudu maso yammacin Najeriya ya ce, ƴan damfara na amfani da ire-iren waɗannan shafuka don su tattara bayanan jama’a. Su kuma saida bayanan, wanda hakan zai sa a iya kai wa mutum hari ta yanar gizo. 

Sashen shari’ah na Amurka ya musanta da’awar 

An ruwaito cewa daraktan kafofin watsa labarai a ofishin babban mai shari’ah a Amurka na gundumar California, Mrozek Thom, ya musanta da’awar

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.