Back to Africa Check

Ɗan siyasa daga jam’iyyar adawa Omoyele Soworo baiyi barazanar zai kulle shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba

A taƙaice: An danganta wasu maganganun waɗanda ke kai farmaki ga Omoyele Soworo na jam’iyyar African Action Congress, waɗanda ke cewa ya ce zai ɗaure shugaban ƙasar Najeriya Buhari. Sai dai babu wata hujjar da ta tabbatar da cewa Soworo ya faɗi wani abu makamancin hakan.

Wani saƙo a Facebook da ke ta yawo a Najeriya na cewa Omoyele Soworo ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar African Action Congress (AAC), na cewa “Zan ɗaure Buhari idan na zama shugaban ƙasa a 2023”. 

Sowore mai fafutukar kare hakkin bil adama ne a Najeriya, mai yaƙin ganin cigaban demokaraɗiya kuma mamallakin gidan jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters

A zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, Soworo a ƙarƙashin tutar AAC, ya fito adawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai ya tashi da kuri’u 33,953 daga cikin kuri’u 28,614, 190 da aka kaɗa, yayin da Buhari ya lashe da kuri’u 15, 191, 847. 

A watan Agustan 2019, an kama kuma an tsare Soworo dalilin haɗa zanga-zangar #RevolutionNow. An kuma tuhume shi da laifin cin amanar ƙasa kafin a sake shi a ranar 24 ga watan Disemba. 

Gwamnati ta ƙara tuhumar Soworo da laifin shirya makircin cin amanar ƙasa da zagin Buhari a wata tattaunawa. 

Da’awar 5 ga watan Satumba wadda ta kawo kalaman Soworo na cewa zai ɗaure Buhari, an sake maimaitata a wasu saƙonnin Facebook. 

Sowore ya faɗi waɗannan kalamai, waɗanda ka iya sawa a sa ke tsare shi? Mun bincika. 

Sowore_False

Babu hujjar da ta tabbatar da waɗannan kalamai

Ainihin saƙon bai bayyana waje da lokacin da Soworo ya faɗi kalaman ba. Wannan alamun tambaya ne, waɗanda ke tabbatar da cewa ƙirƙirar da’awar da ke yawo a kafafen sada zumunta akayi. 

Babu wani rahoto a manyan gidajen jarida na cewar Soworo ya furta waɗannan kalamai, ko wani abu mai kama da son ɗaure Buhari. 

Idan akayi la’akari da tarihin Soworo, irin waɗannan kalamai dole ne a sa me su a rahotonnin ingantattun gidajen jarida. 

Mun kuma binciki sahihin shafin Soworo na Tiwita, amma ba mu samu wani abu makamancin waɗannan kalamai ba. 

Africa Check na cigaba da samun ƙaruwar kalamai da tsokaci ire-iren waɗannan da ake dangantasu ga manyan ƴan siyasa, yayin gabatowar zaɓen Najeriya na 2023. Irin waɗannan kalaman ƙarya zasu iya gurɓata muhawarar siyasa a yanar gizo. Waɗannan kalamai da aka ƙirƙira aka dangantasu ga jam’iyyar adawa ɗaya ne daga cikin misalan hakan. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.