Back to Africa Check

Ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki Bola Tinubu bai janye daga takara ba

A TAƘAICE: Mun ta cin karo da labaran ƙarya masu tarin yawa da ke ta yawo a shafukan sada zumunta a Najeriya tun bayan mai sa ran yin shugabancin Najeriya Bola Tinuba shiga takara a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki a watan Janairun 2022. Kamar sauran da’awowi da dama, a kwanan nan ma, jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya janye daga takara, ƙarya ce.

“Bola Ahmed Tinubu zai janye daga takarar shugaban ƙasa saboda dalilan da suka danganci lafiya,” wani saƙo da aka yaɗa a wani guruf a Facebook da ke ɗauke da mutane sama da 46,000 ya fara da cewa. 

Saƙon na iƙirarin cewa Bola Tinubu  zai fita daga cikin ƴan takarar zaɓen Najeriya na shekarar 2023 bisa shawarar likitan sa, wanda ya ce ya ajiye buƙatar sa na son yin shugabancin ƙasa saboda lafiyarsa. 

Rubutun na cewa: “Likitocin da ke kula da lafiyar ɗan takarar shugaban ƙasar da bashi da cikakkiyar lafiya daga jam’iyyar APC Mr Yekini Amoda (da aka fi sani da Bola Ahmed Tinubu), likitocin sun bashi shawarar janye takarar son zama shugaban ƙasa daga yanzu.”

Rubutun ya ce ya samo labaran ne daga kamfanin dillancin labarai na Reuters

Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa ne daga jam’iyya mai mulkin Najeriya All Progressives Congress (APC), ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar babban zaɓen ƙasar na 2023. Ya taɓa yin gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya. 

Tun lokacin da Tinubu ya bayyana ƙudurinsa na yin takarar shugabancin ƙasar a watan Janairun 2022, ake ta hasashen ainihin shi waye da kuma yanayin lafiyarsa

A ranar 29 ga watan Satumba, kwana guda bayan fara yaƙin neman zaɓe a ƙasar, ƴan takarar shugabancin ƙasar sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya, wadda sukayi a birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Amma rashin zuwan Tinubu wajen sanya hannun ya assasa jita-jitar da ake akan lafiyarsa. 

Mun samu wasu rubuce-rubucen akan janyewar Tinubu daga takarar a Facebook a nan, nan da nan

Amma waɗannan jita-jita gaskiya ne? Mun bincika. 

Tinubu_False 4

‘Da ƙarfinsa da lafiyarsa, kuma a shirye ya ke don hidimtawa jama’a’

Binciken da mukayi a shafin Reuters na yanar gizo ba mu ga inda aka kawo rahoton janyewar Tinubu ba daga takara. 

A ranar 2 ga watan Oktoba, Bola Tinubu ya wallafa a sahihin shafin sa na Tiwita, yana ƙaryata da’awar cewa ya janye takara. 

Ya rubuta kamar haka: “Da dama sun ce na mutu; wasu sunyi iƙirarin cewa na janye daga yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa. Sai dai  ….. Ba haka ba ne. 

Ya ce yana nan da ƙarfinsa da lafiyarsa, a kuma “SHIRYE ya ke ya hidimtawa ƴan Najeriya daga ranar da zai hau”. Ɗan shekaru 70 ɗin, ya saka hotonsa da ya ɗauka yana kan keken motsa jiki. 

A ranar 10 ga watan Oktoba a Abuja, Tinubu ya ƙaddamar da ɓangaren mata na yaƙin neman zaɓensa. Babu wata alama da ta nuna cewa yaƙin neman zaɓen nasa na ja da baya. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.