Back to Africa Check

Ɗan takarar shugaban ƙasa Sowore Omoyele bai ce zai halasta ‘shan tabar wiwi ba’, magana ce da ta fita daga muhallinta

A taƙaice: Wasu kalamai da aka danganta su ga ɗan siyasar Najeriya daga jam’iyyar adawa Omoyele Sowore an ce ya ce zai halsta shan “tabar wiwi” idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Duk da cewa yana goyan bayan noma ganyen wiwi don cigaban tattalin arziƙin Najeriya kuma yayi bayyana hakan, amma ba mu samu wata hujja da ta tabbatar da cewa yana fafutukar a halasta shan tabar wiwi ba.

Wani saƙo a Facebook ya ambaci ɗan takarar shugaban ƙasar daga jam’iyyar Africa Action Congress (AAC) a zaɓen Najeriya na watan Fabrairun 2023, yana cewa “Zan halasta shan tabar wiwi idan an zaɓe ni a matsayin shugaban ƙasa”. 

Omoyele Sowore ɗan Najeriya ne mai fafutukar kare hakkin bil adama, mai yaƙin cigaban siyasa kuma mamallakin gidan jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters.

Sowore ya magantu akan ra’ayin sa akan halasta ganyen wiwi a Najeriya tun shekarar 2018. Ganyen wiwi ko “wiwi” ita ce bushashen ganye, fure, saiwa da ƴa’ƴan itacen wiwi na cannabis sativa. 

Ya ce zai “mai da ƙasar cibiyar fataucin ganyen wiwi idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa”. Ya tabbatar da cewa ƙasashe da dama na samun maƙudan kuɗaɗe ta hanyar fitar da itacen. 

A watan Oktoba 2022, Sowore ya ce za’a iya amfani da ganyen wiwi wajen yin magunguna, yaduka da abun yaɓawa a gini, ba lalle sai sha ake kawai ba. 

An maimaita da’awar 14 ga watan Oktoba 2022 a wasu saƙonnin Facebook. 

Shin Sowore ya ce zai halasta shan wiwi? Mun bincika. 

Soworeweed_missing vontext


Magana ce da aka yi ta ba a muhallinta ba

Ganyen wiwi har yanzu abu ne da aka haramta amfani da shi a Najeriya, an sha yin mahawarori akan halasta shi. An ta jayayya akan masu so da marasa so a halasta shi. 

Kasancewar Sowore na takarar zama shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairun shekarar 2023, rubutun da za’a wallafa a ce ya ce zai halasta shan ganyen wiwi zai iya jawo masa cece kuce. 

Ba’a samu wani babban gidan jaridar da ya bada rahoton wannan maganar ba. Mun kuma bincika “halasta shan tabar wiwi” a duk tattaunawar da yayi bamu samu inda yayi wannan furucin ba. Alamu sun nuna cewa furucin sa aka ɗauka aka fitar da su daga muhallinsu ko kuma ma ƙirƙirar su akayi. 

Sowore ya ce zai halasta ganyen wiwi idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, wanda ya ce hakan hanya ce ta samar da kuɗaɗe a ƙasar. Amma dai bai ce zai halasta “shan tabar wiwi”.

 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.