Back to Africa Check

Ganyen shuwaka, ganyen lemongiras da citta basa maganin zazzaɓin cizon sauro

“ Maganin zazzaɓin cizon sauro mai naci,” taken wani saƙo da ke ta yawo a Facebook a Najeriya.

Saƙon na cewa haɗa ganyen shuwaka, lemongiras da citta zai magance zazzaɓin cizon sauro mai naci ko wanda yaƙi jin magani.

“ A wanke ganyayyakin da aka ambata tare da citta sai na a dafa na tsahon mintuna ashirin. A bar shi ya huce sai aringa shan kofi ɗaya sau uku a rana har tsahon sati guda,” rubutun ya ce.

Zazzaɓin cizon sauro wanda akafi sani da maleriya cuta ce da cizon sauron da akafi sani da anopheles ke jawowa. Zazzaɓin kan zama hatsari ga rayuwa idan aka yi sakacin shan magani.

Shin wannan haɗi na maganin zazzaɓin cizon sauro mai naci?

 

recurring malaria

 

‘ Ku ziyarci likita, ayi muku gwaji a baku magani’

Hukumar lafiya ta duniya tace sama da mutane 400,000 ke mutuwa sanadiyar zazzaɓin, bayan kuma za'a iya maganin zazzaɓi a kuma kare kai daga kamuwa da zazzaɓin. Hukumar lafiyar ta ƙara da cewa gane cutar da wuri da kuma samun kulawar da ta dace zasu hana zazzaɓin zama barazana ga rayuwa.

Okon Essien, Farfesa a sashen koyan aikin likitanci na jami'ar Calabar a Najeriya  ya ce, “babu wani nazari na a kimiyance da ya tabbatar da cewa haɗin na maganin zazzaɓin.

“ Ni dai ba zance a sha wannan ba, haka nan ban tabbatar da sahihancin sa ba,” Farfesan ya shaidawa Africa Check. “ Akwai magungunan cutar da aka amince da su kuma aka jima ana amfani da su, muna da su ako da yaushe kuma basu da tsada. Ban ga dalilin da wasu zasu nemi wannan hadi don maganin zazzaɓin.”

Farfesan ya bada shawarar duk wanda ya ke zaton ya kamu da zazzaɓin da su je asibit a ɗauki jininsu don gwaji ko suna ɗauke da cutar.

“ Don tabbatar da cewa ba wata cutar suke ɗauke da ita ba, daga nan sai a basu maganin da ya dace,” Farfesan ya ce.

A kwanan nan Africa Check ta tantance da'awa makamanciyar wannan da ta ce shan shayi mai ɗauke da lemongiras da citta na wanke dauɗar jiki.

 

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.