Back to Africa Check

Garin ganyen gwanda da man kaɗanya ba zasu magance maƙoƙo ba

Haɗa garin ganyen namijin gwanda da man kaɗanya zai cire maƙoƙo, a cewar wani saƙo da ke yawo a Facebook a Najeriya.

“ A shafa safe da yamma don kawar da maƙoƙo gaba ɗayan sa,” saƙon ya ce.

Shin hakan zai yi aiki? Mun bincika

Goitre_remedy

 

Yanayin maganin ya danganta da abun da ya jawo maƙoƙon

Maƙoƙo shine kumburin tairoyid gilan mara raɗaɗi a cikin wuya.

Ƙarancin sinadarin ayodin a cikin abinci ke jawo shi. A wasu lokutan yana ɓacewa da kansa ba tare da magani ba. Ga wasu kuma zai kasance matsala babba da ke ɓukatar maganin asibiti.

Abubuwan da ke jawo maƙoƙo da kuma matsalar da ya ke haifarwa sun haɗa da ƙarancin sinadarin ayodin, matsalar garkuwar jiki, jima’i da shekaru- mata da mutanen da suka haura shekaru 40 su fi zama cikin barazanar kamuwa da cutar- haka nan masu juna biyu, matan da suka daina al’ada da kuma yawan kasancewa cikin matsanancin haske.

Mun tuntuɓi Aihanuwa Eragie, Farfesa a fannin magunguna na jami’ar Benin akan maganin cutar.

“ Akwai abubuwa da dama da ke jawo maƙoƙo, a kimiyance ba yadda za’ayi a ce ka shafa abu ace kuma ciwo ya fice,” a cewar Farfesar.

“ Ana maganin ciwon ta hanyar bada magunguna ko kuma a cire a asibiti.”

Hukumar kiwon lafiya ta Britaniya ta bada shawarar a tsaya a ga gudun ruwan ciwo ga waɗannan maƙoƙon ya kasance ɗan ƙarami ne kuma baya bada matsala. Maganin maƙoƙo dai ya danganta da abun da ya jawo shi.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.