Wani saƙo dake yawo a Facebook da WhatsApp a Najeriya na cewa ana cigaba da cike takardar neman “tallafin” gwamnatin tarayya na ƙanana da matsakaitan sana’oi (MSME).
“Ana cigaba da shirin tallafin Gwamnatin tarayya ga ƙanana da matsakaitan sana’oi a Najeriya,” saƙon ya ce.
Saƙon ya haɗa da takardar bayanin yadda za’a nemi tallafin da kuma waɗanda zasu iya neman tallafin. Da kuma link na shafin yanar gizon da za’a je don neman tallafin.
Har yanzu Najeriya na bada tallafin MSME? Mun bincika.
An rufe shirin
Link ɗin na kai mutum wani shafi da ke ƙunshe da taken “Shirin tallafi na MSME 2021 | survivalfund.gov.ng/“. Ya kuma bayyana URL na shiga shafin neman tallafin na gwamnati.
Africa Check ta binciki shafin da gwamnati ta tanada don yin rijistar samun tallafin amma ta tarar an riga an rufe neman tallafin.
Ofishin gudanar da aikin tallafin sun fitar da sanarwa a shafin su na Facebook, haka nan an ruwaito a kafafen watsa labarai cewa za’a buɗe neman tallafin ranar 27 ga watan Junairu 2021 zuwa 2 ga watan Fabrairu 2021 a jihohi 30 da basu gama karɓar kasonsu ba.
An rufe neman tallafin gwamnatin tarayya na MSME. Saƙonnin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa har yanzu ana iya neman tallafin ƙarya ne.
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment