Back to Africa Check

Hoton da aka sauyawa fasali na iƙirarin cewa an bayyana mai girkin nan ƴar Najeriya a matsayin wadda ta ci gasar girki ta Guinness ta duniya

Hoton da aka sauyawa fasali na iƙirarin cewa an bayyana mai girkin nan ƴar Najeriya a matsayin wadda ta ci gasar girki ta Guinness ta duniya.

Wani rubutu da aka wallafa a Facebook na iƙirarin cewa, a hukumance an tabbatar da mai girke-girke Hilda Bassey a matsayin wadda ta lashe gasar Guinness world of records. 

Rubutun wanda aka rarraba shi a shafuka da guruf na Facebook, ya haɗa da hoton Bassey tana riƙe da abun da yayi kama da takardar shaida daga Guinness World Records. 

Bassey wadda aka fi sa ni da Hilda Baci, ta kammala “gasar girke-girke” a Mayu 2023, don ta zama wadda tafi kowa daɗewa tana girki ba tare da tsayawa ba a duniya. 

“Yanzu ta tabbata a hukumance. An bayyana Baci a matsayin wadda ke riƙe da shaidar Guinness World Records,” a cewar ɗaya daga cikin rubuce-rubucen

“Hilda Baci ta ƙarɓi takardar shaidar itace wadda tafi kowa daɗewa tana girki daga Guinness World Records,” wani rubutun ke iƙirarin cewa.

A rarraba a wasu rubuce-rubuce a wasu shafuka kamar a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan ,nan da nan.
 

Hilda_Fake

Har yanzu Guinness na nazarin wannan ƙokari da Bassey tayi 

A lokacin da Bassey ta ke wannan ƙokari, Mai girke-girke Lata Tondon ƴar ƙasar Indiya ce ta kasance wadda tafi kowa dadewa tana girki a duniya, inda ta shafe awanni 87 da mintuna 45 tana girki babu tsayawa a shekarar 2019. 

Gasar girkin na Bassey ya ɗauki tsahon awanni 100 daga ranar Alhamis 11 zuwa ranar Litinin 14 ga watan Mayu 2023. 

Sai dai kuma ƙokarin na ƴar shekaru 27 ɗin ba’a tabbatar da shi a hukumance ba lokacin da aka fara yaɗa sakonnin kafafen sada zumuntar. 

A wata sanarwa da suka wallafa a shafin su na yanar gizo a ranar 16 ga watan Mayu, Guinness World Records sun ce, suna fatan tawagar masu tantancewarsu zasu tantance ƙokarin Bassey nan ba da jimawa ba. 

“Muna sane da yunƙurin da Bassey tayi,  kuma muna sa ran ƙarɓar hujjoji don tawagar masu gudanarwa mu su duba kafin tabbatarwa a hukumance,” a cewar sanarwa da ta fito daga mai magana da wayunsu. 

Binciken kafar tantance hoto ta TinEye ya nuna hoton yayi kama da wasu hotuna da aka ɗora a yanar gizo tun watan Afrilun 2020. Kafar binciken hoto ta Google itama ta nuna cewa hoton wani mai fasahar sauya hoto ne ya ɗora shi a Tiwita. 

Hoton Bassey da ke yawo a yanar gizo riƙe da takardar shaidar Guinness World Records an sauya shi ta hanyoyin sarrafa hoto da nau’ra. 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.