Back to Africa Check

Hoton titi a Pakistan ne, ba titin Ughelli-Asaba da ake aiki a Najeriya ba ne

ATAƘAICE: Wani hoton na ta yawo a Najeriya. Wanda ke cewa aikin babban titin Ughelli da Asaba da ke jihar Delta ne da aka kammala, aka kuma ɗora alhakin ginin titin ga gwamnan jihar Ifeanyi Okowa. An yi haka ne don a ƙara fito da gwamnan, saboda takarar shugabancin ƙasar da ya ke son yi a zaɓen 2023. Hoton, na wani babban titi ne a Pakistan ba Najeriya ba.

 

An saka wani hoto a wani guruf na Facebook Najeriya a watan Satumba 2022 da ke iƙirarin cewa babban titin Ughelli zuwa Asaba da ke jihar Delta, kudancin Najeriya ne aka kammala.

Taken da ke tare da hoton na cewa; ‘Mun gode gwamna Ifeanyi A. Okowa da gaggawar saka hannu da kayi da kuma kammala aikin babban titin Ughelli-Asaba a ƙasa da shekaru 8 da fara aikin ka na gwamna. 

Asaba itace babban birnin jihar Delta, yayin da Ughelli kuma wani gari ne mai nisan kilo mita 170 daga kudu maso yamma.

Ifeanyi Okowa shi ne gwamnan jihar kuma ɗan takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa daga jam’iyyar People’s Democratic Party a zaɓen Najeriya na 2023. Rubutun na Facebook ya haɗe da shafin gwamnan na Facebook.

Aikin babban titin mai ɗauke da hanyoyi biyu, gwamnatin da ta gabata ce ta fara shi ƙarƙashin gwamna Emmanuel Uduaghan a shekarar 2007. Amma an bada umarnin kammala aikin titin a shekarar 2019 ƙarƙashin gwamnatin Owowa.

An sake rarraba hoton tare da da’awar a nan, nan da nan.

Shin hoton da aka rarraba a shafukan sada zumunta na titin Ughelli-Asaba ne da aka kammala? Mun bincika.

HighwayNigeria_False

Hoton titin motoci na Hazara ne da ke Pakistan

Binciken hoton da kafar tantance hotuna ta Google reverse image search ya kai mu matattarar wasu hotuna da aka tattara ranar 20 ga watan Satumba 2020 a shafin Pinterest wanda wani shafin yanar gizo na tafiye-tafiye na Pakistan suka saka. A wajen an nuna hoton a matsayin hoton titin motoci na Hazara a ƙasar wadda ke Kudancin Asia wato Pakistan

Da kuma muka binciko “ruwan sama a titin motoci na Hazara”, binciken ya kai mu ga hotunan wannan titin, wanda aka bayyana a matsayin titin mota na Hazara. 

An fara aikin titin mai tsahon kilomita 180 a shekarar 2014, an kuma gama ginin aka kuma ƙaddamar da shi a tsakiyar 2020

A watan Fabrairun 2022, Nigerian news ta kawo rahoton zanga-zangar da masu bin titin Ughelli- Asaba sukayi don kokawa da yadda aka ƙi gyara titin. Amma bamu samu wani sabon rahoto akan aikin titin ba, ko rahoton cewa an kammala aikin titin.

Hoton da ke yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya ba ya ɗauke da hoton titin Ughelli-Asaba, kuma ba a Najeriya aka ɗauki hoton ba. Ba’a kammala babban titin Ughelli da Asaba da ke jihar Delta ba. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.