Back to Africa Check

Hukumar kula da kaɗaɗen shiga ta ƙasa bata ɗaukar ma’aikata

Wani saƙo da aka saka a Facebook Najeriya na iƙirarin cewa hukumar kula da kuɗaɗen shiga ta ƙasa, wadda akafi sani da Firs na ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022-23. 

Sakon na cewa: “FIRS sun fara ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022/2023. Saƙon ya bayyana hanyoyin da ya kamata ku bi don taimaka muku ku samu sunan ku ya fito a cikin shirin ɗaukar ma’akatan hukumar kula da kuɗaɗen shiga na bana.”

Sannan aka bada wani wajen latsawa da mutum zai latsa ya shiga, don “ƙarin sanin cikakken bayanin yadda za’a nemi aikin”. Mun samu da’awowi makamantan wannan, wanda wajen latsawar ke kai mutum wani shafi na daban, a nan da nan

Firs ce ke da alhakin tarawa, shigarwa da lissafa kuɗaɗen haraji da sauran kuɗaden shiga na Najeriya, ƙasar da tafi kowacce ƙasa girman tattalin arziƙi a Afrika. Shin suna ɗaukar ma’aikata? 

FIRS_False

Ba’a ɗaukar ma’akata a hukumar kula da haraji

Babu hujjar da ta nuna cewa ana ɗaukar ma’aikata a shafin hukumar na yanar gizo, shafin su na Tiwita ko shafin su na Facebook

A ranar 1 ga watan Agusta Firs ta wallafa wata sanarwa a shafukanta na Tiwita da na Facebook, suna gargaɗin jama’a akan su kiyayi ƴan damfara, sannan suka ce basa ɗaukar ma’aikata. 

“Hukumar na son ta jaddada cewa bata ɗaukar ma’aikata a halin yanzu, sannan bata taɓa ɗaukar ma’aikata ta bayan gida ba,” sanarwar ta ce.


Ta kuma gargaɗi gidajen jarida da su guji wallafa shafuka ko sanar da hanyar neman aiki wadda hukumar bata da masaniya akai, ko kuma waɗanda suka kasance na bogi a shafukan su.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.