Back to Africa Check

Jirgi bai faɗi yayin da zai sauka a Legas, Najeriya ba- jirgin da ake son gyarawa ne ake janyewa

Bidiyon jirgin da bashi da fuka-fukai akan hanya mai cike da ababen hawa ya yawata a kafafen sada zumunta a Najeriya, aka kuma yi iƙirarin cewa jirgin sama ne ya faɗo yayin da zai sauka akan titi kusa da tashar jiragen sama ta ƙasa da ƙasa ta Murtala Mohammed da ke Ikeja, Legas.

An kuma wallafa da’awar a wasu shafukan watsa labarai a ƙarshen watan Mayu 2022. 

Amma meye gaskiyar labarin? 

Crashland_ False
 

Hukumomi sun ƙaryata da’awar

Hukumar tashoshin jiragen sama ta tarayya(FAAN), hukumar gwamnati da ke da alhakin kula da tashoshin jiragen sama a ƙasar, ta ƙaryata da’awar. 

FAAN ta ce a ranar 24 ga watan Mayu a wani rubutu da suka wallafa a Facebook ga jama’a “ayi watsi da labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an samu fadowar jirgi a tashar jirage ta Ikeja. Mamallakin jirgin ne ya sayar da jirgin, yana kuma ƙoƙarin kai jirgin inda aka saya”. 

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ma ta ƙaryata da’awar, inda ta ce “babu abun da ya faru”, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

Babu alamun faɗuwar jirgi

Jirgin da ke cikin bidiyon bai nuna alamun cewa faɗuwa yayi ba, sannan daga gani an cire fuka-fukan jirgin a tsanake.

A wasu sakonnin Twita, wani mai nazari akan jiragen sama Daniel Dikio ya ce jirgin samfurin Airbus A319 ne, kuma an cire fuka-fukan sa ɗaya bayan ɗaya a tsanake.

“Hakan kuma ba zata faru ba idan jirgin faɗowa yayi, cire fuka-fukan na nuna alamun cewa ciccire kayan jirgin ake. Jikin jirgin bai ɓaci ba, wanda hakan ba zai taɓa yiwuwa ba idan da abun da ake zato ne na cewa jirgin faɗowa yayi.”

“Nayi nazarin bayanan jirgin sama, ban samu wani abu na daban ba. Kuma duka jiragen A319 da ke aiki a Najeriya a lissafe suke a lissafin da nayi, Dikio ya rubuta a sakon na twita.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.