Back

Kada ku kula da almarar ‘sabon shirin ɗaukar aikin ƴansanda 2022’ da ke yawo a yanar gizo

A TAƘAICE: Hukumar ƴansandan Najeriya ta nesanta kanta da wata sanarwa da ke yawo a yanar gizo dangane da ɗaukar aiki a hukumar na shekarar 2022. Hukumar ta buƙaci jama’a da suyi burus da sanarwar. 

 

Wani saƙo da ke yawo a Facebook a watan Yuli 2024 na iƙirarin cewa Hukumar ƴansanda ta Najeriya (PSC) ta wallafa sabunta shirin ɗaukar ma’aikata na 2022. 

A matsayinsu na masu saka ido, hukumar itace ke kula da mu’amullar jama’a da ƴansanda. 

Wani bangare na saƙon na cewa: “Ana bawa waɗanda suka samu nasara shawarar da su buga takardar kira da suka sabunta, sai su garzaya zuwa Kwalejin ƴansandan da aka rubuta a takardar tare da sunayensu. Za’a horar da ma’aikatan ranar Litinin 22 ga watan Yuli 2024. 

Sanarwar na da kwanan watan 6 ga watan Yuli 2024, wani “Ikechukwu Ani, shugaban yaɗa labarai da hulda da jama’a ne ya sa hannu”.

Za’a ga kwatankwacin da’awar a nan da nan. ( A lura: Za’a bayyana wasu wuraren da aka wallafa da’awar a ƙarshen wannan rahoton.) 

Shin wannan sanarwar daga ƴansandan ta fito? Mun bincika. 

Nigeriapolice_false

‘Rubutun almara ne’

An samu saƙonnin zamba da dama a baya a Facebook da aka alaƙanta su ga ƴansandan Najeriya. 

Ranar 12 ga watan Junairu, mun tantace wata da’awa da ke cewa ƴansandan sun wallafa “adadin waɗanda suka ɗauka aiki na musamman”. Wannan dai ƙarya ce. 

A ranar 9 ga watan Yuli, hukumar ta musanta da’awar da ke iƙirarin samun aiki na shekarar 2022 a wata sanarwa, wadda ta bayyana da’awar a matsayin “almara”. 

“Hukumar bata taɓa bawa mutane shawarar su buga wata takardar gayyata da aka sabunta ko su je makarantun horar da ƴansanda ba. Bata kuma bayyana wata ranar fara shirin horarwa ba. Kuma bayyana ranar Litinin 22 ga watan Yuli da akayi a saƙon na Facebook, tunanin wanda ya wallafa rubutun ne,” cewar hukumar. 

Hukumar ta bawa masu “sha’awa shawarar su yi hakuri su jira sanarwarta a hukumance akan shirin ɗaukar aikin da aka kammala.”

An wallafa irin da’awar a nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan

 

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.