A TAƘAICE: Wani rubutu a kafafen sada zumunta na cewa kamfanin siminti na Dangote sun rage farashin buhu guda na simintin da kashi 50%. Kamfanin sun ce ba haka ba ne.
“Yanzu-yanzu: SIMINTIN DANGOTE YANZU N2700 NE DAGA 1 GA WATAN OKTOBA, 2023. Dangote ya bayyana sabon farashin siminti da ya karye da kashi 50% daga ranar 1 ga watan Oktoba inda ya koma daga N5500 zuwa N2700,” cewar wani rubutu da aka wallafa a Instagram.
Kamfanin Dangote Cement Plc na daga cikin manya kamfanin da ke yin siminti mafi girma a Africa, kamfanin na da hedikwata a Legas, Najeriya. Ɗaya ne daga cikin rukunin kamfanin Dangote Group, wanda biloniya Aliko Dangote ya mallaka.
Rubutun ya samu masu so har 1,300 da masu tsokaci har mutum 170.
Mun ci karo da makamanciyar da’awar a Facebook a nan, nan, nan da nan, sannan a Instagram ma a nan, nan, nan, nan da nan.
Dangote Cement sun karya farashin siminti? Mun bincika.

‘Labaran Ƙarya ne’
A watan Agusta 2023, kamfanin ya shaidawa gidajen jarida cewa farashin siminti yana kamawa tsakanin N4,010 zuwa N4,640.
Ya kuma bayyana cewa farashin buhun siminti zai iya kaiwa har N5,300 idan an ƙara da kuɗin ɗaukar kaya. .
Dangote sun musanta da’awar ta tafafen sada zumunta, wadda mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejine ya kira da “labaran ƙarya”.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment