Back to Africa Check

Ƙasar Canada bata bada muhalli ƙyauta ga baƙin haure

“Ɗaukar ma'aikatan gwamnatin Canada na shekarar 2022,” kanun wani saƙo da ke yawo a WhatsApp a Najeriya. 

An watsa saƙon a wasu shafukan kafar sada zumunta ta Facebook ma. 

Saƙon ya haɗa da link ga wanda ke buƙatar komawa zama ƙasar Canada. Sannan saƙon ya umarci masu so dasu kasance sun kai shekaru 16 zuwa sama, ya zamana kuma suna jin harshen turanci. 

Saƙon yayi iƙirarin gwamnatin Canada ce ke ɗaukar ma’aikatan, kuma shirin ya haɗa da kuɗaɗen tafiya, muhalli da “kayan kiwon lafiya”.

Hakan gaskiya ne? Mun bincika.

Canada_visa

Da alama ɗamfarar yanar gizo ce

Link ɗin na kai mutum wani shafi mara tsari, inda ake umartar waɗanda suka ziyarci shafin da su bada bayanin inda za’a same su.

Rubutun da ke shafin yana cike da kurakuran da suka saɓawa ƙaidar rubutu, alamar cewa ba ƙwararru bane suka tsara shafin, waɗanda su ne ya kamata ace su ke isar da saƙon gwamnatin ƙasar. 

Duk da cewa manema labarai sun ruwaito cewa gwamnatin Canada na shirin karɓar baƙin haure har 431 ,645 a shekarar 2022 a matsayin mazauna ƙasar na dindindin, amma dai babu wata kafar sadarwar ƙasar da ta ruwaito cewa gwamnatin na shirin ɗaukar ma’aikata ƴan ƙasashen waje guda 450,000. 

Sahihin shafin tiwita mallakin ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya bai bayyana bayanin ɗaukar ma’akata a ƙasar ba.

A watan Satumbar 2021, gwamnatin Canada ta wallafa wani rubutu da ke gargaɗin baƙin haure da su kiyayi ƴan damfara, sun kuma bayyana yadda za’a iya gane shafukan ƴan damfara.

Duk alamu sun nuna cewa wannan damfara ce aka shirya don samun damar ɗaukar bayanan jama’a. Ba shi kuma da alaƙa da gwamnatin ƙasar Canada ta kowacce hanya.

Don samun hanyoyin gane ƴan damfara a yanar gizo, a karanta bayanin hanyoyin gane su da mu kayi a nan

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.