Back to Africa Check

A kiyayi damfara- babban bankin Najeriya baya bada kuɗin eNaira na biliyan 50

Wani rubutu da ke yawo a WhatsApp da Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa babban bankin ƙasar na rabawa jama’ar ƙasar Naira billiyan 50. 

A cewar rubutu da aka buga a ranar 26 ga watan Oktoba 2021, kawai ƴan ƙasar da suka sauke suka kuma yi rigista da jakar sabon kuɗi ta eNaira a yanar gizo ne zasu samu kyautar kuɗin. 

Sabon kuɗi na yanar gizo na eNaira, kuɗi ne na dijital da babban bankin Najeriya CBN ya ƙaddamar ranar 25 ga watan Oktoba. Rubutun ya ce “babban bankin na ƙoƙarin ganin cewa eNaira ta samu matuƙar karɓuwa”.

Rubutun ya ƙunshi hoton shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele suna riƙe ƙaton hoto ɗauke da alamar eNaira.

Shin da gaske ne za’ayi rabon Naira biliyan 50?

Nigeria_bank_scam

Alamomin dafara ta yau da kullum a yanar gizo

Amfanin da akayi da rubutun da ya gaza ƙa’idojin rubutu ya fara nuna cewa rubutun ba daga tushe ingantacce ya fito ba, musamman manya hukumomi. 

Rubutun ya kuma haɗe da wani shafi, da ba shafin babban bankin ba ne ko na eNaira. Adireshin yanar gizo na hukumomin gwamnati na ƙarewa da “. gov.ng”.

A shafin an buƙaci masu nema da su rarraba link ɗin rubutun a WhatsApp don samun eNaira ta 50,000.

Wannan misali ne na yadda ƴan damfara ke yi a Facebook don samun yawaitar masu zuwa ga rubutun su. A lokuta da dama wannan na daga cikin alamomin da ke tabbatar da ƙaryar talla.

Za ku iya karanta hanyoyin da muka zayyano akan yadda zaku gano ƴan damfara a Facebook a nan

‘Ƴan damfara sun ƙara kunno kai.’ cewar CBN

Bankin sun ƙaryata wata alaƙa da ƙyautar.

“Wannan ba gaskiya ba ne, kuma ma ba zai zama gaskiya ba. CBN bata taɓa kuma ba zata taɓa raba kuɗi ga kowa ba,” Osita Nwanisobi, daraktan sadarwa na CBN, ya shaidawa Africa Check.

“Zamu iya samar da bashi ga jama’a, kuma zasu iya neman bashin ta bankunan da ke bada bashin akan kuɗin ruwa madaidaici.”

“ Ƴan damfara sun ƙara kunno kai,” cewar Isa Abdulmumin shugaban sashen watsa labarai na babban bankin.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.