Back to Africa Check

Lemon tsami baya maganin cutar sankara— a nemi maganin asibiti

A TAƘAICE: Wani rubutu a Facebook da ke yawo a Najeriya na iƙirarin cewa ruwan lemon tsami na maganin cutar sankara. Ƙwararru sun ce ba haka ba ne.

Wani bidiyo da ke yawo a Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa haɗa ruwan lemon tsami da ruwa zai iya maganin kowanne nau’i na cutar sankara. 

Mutumin da ke cikin bidiyon, wanda aka yi shi ranar 28 ga watan Mayu 2023, na bawa masu kallo umarni a harshen Igbo da Turanci da a saka lemon tsamin da aka ɓare a cikin kofin ruwan ɗumi. Mutumin ya ce za’a iya shan haɗin sau biyu a rana, safe da yamma na tsahon watanni uku. 

Sankara, cuta ce da ke haddasa tsurowar wata ƙwayar halitta da ta ke bazuwa zuwa wasu sassan jiki. 

An kalli bidiyon a ƙalla sama da sau 57,000. Sannan an yi irin wannan da’awar a wasu wuraren a Facebook, kamar a nan, nan da nan. 

Akwai wata hujja da ta tabbatar da cewa ruwan lemon tsami na maganin sankara? Mun bincika. 

Limecancer_false

Amfanin lemon tsami

Lemon tsami na da sinadarin bitamin C mai yawa, sinadarai masu samar da antioksidan da sauran abubuwa masu amfani ga jiki. Dangane da haka, za’a samu ƙarin ingancin garkuwar jiki da kuma raguwar hatsarin kamuwa da ciwon zuciya, a cewar shafin yanar gizo na Healthline mallakin ƙasar Amurka. 

Shafin ya ƙara da cewa ruwan lemon tsami na da sinadarin alkaline mai yanayin pH 8 zuwa sama. 

Ana amfani da haidurojin wanda ake kira pH don nuna yawan sinadarin asid ko alkaline na abu. Ana auna komai a ma’auni daga 1 (mafi yawan haidirojin da asid) zuwa 14 (mafi ƙanƙantar haidirojin da alkaline ko “asali”). Sassan jiki daban-daban na da mabambantan yanayin pH don samun damar yin aiki yadda ya kamata. 

Africa Check ta taɓa tantance da’awowin da ke iƙirarin cewa za’a iya magance cutar sankara ta hanyar sanya jiki ya zama yana da ƙarancin asid da kuma yawaitar alkaline. Sai dai waɗannan da’awowi sun saɓawa manyan hanyoyin kimiyar jiki, kamar misalin yadda ake daidaita asid wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen samun lafiya ingantacciya. 

Kamar yadda Healthline ta bayyana babu wata hujja a kimiyance da ta tabbatar da da’awar da ke cewa ruwan alkaline zai iya magance, kiyaye da kuma warkar da cutar sankara. 

Ba zai warkar da cutar sankara ba- Ƙwararre

“Shan ruwan lemon tsami baya warkar da sankara,” Abidemi Adenipekun, Farfesa akan magani da haske da kuma cutar sankara a jami’ar Ibadan, ya shaidawa Africa Check. 

Ya ce rubutun ya kasance wanda akayi shi akan yarda da cewa idan an mai da wajen zaman ƙwayoyin halitta ya zama yana da alkaline mai yawa ba zai bar cutar sankara ta sake a wajen ba. 

Wasu binciken sun nuna cewa yawan asid a cikin ƙari na sa ya ƙara yaɗuwa, don haka saka ƙwayoyin halittar su zama da alkaline a tattare da su zai taka muhimmiyar rawa wajen magani a nan gaba. Yana da muhimmanci a sani cewa wannan wani canji ne da ke kewayen ƙarin, ba wani sauyi ne da ya danganci jiki ba. 

Waɗannan bincike ba’a yi su don samar da alkaline a muhallin jikin ɗan adam ba. Sannan sauyawa jiki pH zai iya zama hatsari. Abubuwa da dama ne da ke jiki suke gudanar da shi don ganin jikin yana tafiya yadda ya kamata. 

“Ya zamana ana amfani da lemon tsami a matsayin wani sindari ne kawai, ba kuma a ringa shan sa ko da yaushe ba. Waɗanda ke fama da cutar sankara su je su karɓi maganin da ya dace,” Adenipekun ya shaidawa Africa Check. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.